Showing 345001 words to 348000 words out of 641791 words

Chapter 116 - HALYSAAH COMPLETE

03 Sep 2026

246

ma tace "Bana son sake ji

n bakin kowa a cikin ku, ba wannan ne dalilin da yasa na hada ku a nan ba, what is all this nonsense???" A hankali Jawwad yace "There is nothing that will be said to me here da zai yi convincing dina or change my perspective of this whole thing Hajja, don

haka kar ma ace min komai i am not interested, bana bukatar jin komai" Hajja ta saki baki tana kallonsa, zai fita daga parlon tace "Jawwad" Tsayawa yayi amma bai juyo ba, Ajay ya karasa har inda yake tsaye ya zaga gabansa yana kallonsa yace "Halysaah ko? T

ake a chill pill, she is urs.... It's just a matter of time, i am giving you my words" Yana kai wa nan ya fice daga parlon without turning back, Jay ya bi sa da kallo, Hajja was totally speechless a inda take tsaye baki bude, bayan few seconds tace "Allah

ya sauwake, Allah ya tsare mu da wannan ta

ɓ

ara sai kace a garin ga

ɓ

a ga

ɓ

a, shi Jawwad din mahaukaci ne me kuma zai yi da matar da aka aura maka, ko kuma ita Halysaar er gwal ce? meye ma amfanin auro irinta cikin zuri'a tunda ta dalilinta gashi zumunci na n

eman samun tangarda, sam ni yarinyar ma bata min ba saboda abubuwan nan da ke faruwa babu kan gado, shi Jawwad din bashi da hankali ne? Me kuma zai yi da matar ka?" Jay ya juya ya kalli Hajja. Khaleesat ta fito daga Bedroom wajen karfe goma na safe jin sal

laman Yakumbo a parlor, cikin kwantar da murya Yakumbo tace "Ranki shi dade yanxu Yarima ya kirani yace a sanar maki ki shirya za ku yi tafiya yau, ina fatan kin sani" Khaleesat tayi shiru tana kallonta, can tace "To" juyawa tayi ta koma Bedroom din, rabon

ta da ganinsa tun jiya da suka dawo gidan Hajja da yamma, ta zauna kan kujera tayi tagumi tana kallon babban plasma din dakin, ko baccin kirki bata yi ba daren jiya saboda damuwa gashi har ta fara jin kirjinta na ciwo, tana ta zaune har bayan minti talatin

ta ji an bude kofar dakin ta daga kai da sauri, bai ko kalli inda take zaune ba har ya shigo cikin dakin, ta bi sa da kallo har ya dau abubuwan da zai dauka zai fita daga dakin ta hade rai tace "Ina za mu je?" Ba tare da ya kalleta ba yace "Ban sani ba"

Daga haka yayi ficewarsa daga dakin, ta ta

ɓ

e baki ta dauke kanta, bayan fitarsa babu dadewa sai ga Yakumbo ta zo sanar mata ta fito Yarima na jiranta, Khaleesat ta

ɗ

an hade rai tace "To ai ni ban hada kayan ba" Yakumbo ta

ɗ

an yi murmushi tace "To ranki shi

dade idan babu damuwa ki bani izinin in hada maki, Sai ki dinga nuna min duk abinda zaki bukata" Khaleesat tace "A'a kar ki damu Mama zan hada yanxu" Daga haka ta juya ta koma dakin, sai da Khaleesat ta

ɓ

ata kusan minti talatin kafin ta hada duk abubuwan

da tasan zata bukata a akwati, gaba daya jikinta a sanyaye yake duk da tafi zargin Maryland za su koma, But will she cope there without Jay?? tunanin hakan yasa hawaye ya fara sauka idonta, a haka ta fito daga dakin, Yakumbo ta fita da akwatin nata waje Kh

aleesat na biye da ita kamar warce aka zare ma laka, Mikewa Ajay dake zaune daya daga parlor din part din yana jiransu yayi, yana kallon Yakumbo yace "Ki bar akwatin a nan za a shigo a dauka" Da ladabi tace "To ranka shi dade" Ita dai Khaleesat sau daya ta

kallesa ta sunkuyar da kanta, babu yabo babu fallasa yace "Mu je" Bin bayansa tayi fuskarta babu fara'a suka tafi har parlon Mai martaba don yi masa sallama, Mai martaba na kallon Ajay yace "Flight din karfe nawa ne?" Ajay yayi kasa da murya yace "Na dare

ne ranka shi dade" Mai martaba yace "Toh Allah ya kai ku lafiya, idan kun koma sai ka fara mata processing visa din UK, kasan akwai occasion da za ku yi attending a can, if there is anything concerning the Visa processing you let me know" Ajay yace "To in

sha Allah ranka shi dade" Ita dai Khaleesat kanta na kasa tun da suka shigo parlon, Mai martaba ya sa masu albarka suka bar parlon bayan yayi instructing Ajay yaje su ma Aunty sallama. Bayan sun fito bangaren Sarki Ajay ya nufi part din Aunty duk da bai s

o ba but he have no choice, ita dai Khaleesat na biye da shi tana jan kafa, Aunty na zaune parlonta tare da Walid sai Maryam warce bazata wuce 25 years ba Ajay ya shigo parlon tare da Khaleesat, duk suka daga kai suna kallonsu, sosai gaban Khaleesat ya fad

i bayan sun hada ido da Aunty, ta zauna kasan carpet ta gaidata a hankali sannan ta gaida Walid da Maryam, Walid ne kadai ya amsa gaisuwar nata yana kallonta, Maryam kuwa sai danna wayarta take ta toshe kunnenta da Ear pod, Ajay ya zauna kan kujera ya gaid

a Aunty without looking at her, a takaice yace "We are leaving for Maryland..." Da mamaki Aunty tace "You are leaving for Maryland?dama ka saba zuwa yi min sallama ne idan zaka tafi ko kuma rashin kunya ka shigo yi min ka nuna min ai an maka aure?" Ajay ya

ce "Mai martaba ne yayi instructing dina mu shigo mu yi maki sallama so i have no option than to obey his instructions...." Maryam ta kalli uwarta tace "Wai Aunty wannan ce Bazawarar matar da ake cewa dama? Na ganta gidan Hajja jiya na zata irin masu zuwa

kawo kukan su suna neman taimako ne" Ajay ya daga kai ya kalleta, tana ganin haka ta mike daga inda take zaune tana yamutse fuska sanin sai ya iya wanke ta da mari, Aunty ta daure fuska tace "Ina zaki? Ai ba karya kika yi ba Bazawarar ce er matsiyata, sai

ma kin ji history din ubanta..." Ita dai Maryam taki tsayawa a parlon ta nufi kofar wani daki tace "Tabbb wa yaga kwamacala, lallai akwai aiki babba, wai er matsiyata a gidan sarauta, how is that even possible" Daga haka ta shige cikin daki har da sa makul

li, Aunty tace "To karen hauka ya sha da zai ta

ɓ

a ki, meye na shigewa daki kuma, ubanki ne shi da zaki ji tsoronsa?" Walid dai kallon Khaleesat da ta sunkuyar da kanta kawai yake yi kamar ya samu TV, Ajay ya mike yana kallonta a takaice yace "Tashi mu je"

Sai a sannan ta daga kanta hawayen da ya fara taruwa idonta ya gangaro ta mike tana kallonsa, bai kara second biyar a parlon ba ya fice Khaleesat na biye da shi, Aunty ta bi su da wani kallo me cike da tsantsan tsana. Hawaye kawai Khaleesat take bayan sun

bar masarautan, Ajay dai bai ce mata komai ba a bayan motar cause he was also deep in his thought, bayan tafiyar kusan minti talatin driver din yayi horn bakin gate din wani gida bayan an bude gate din ya shiga yayi parking, Ajay ya bude motar ya sauka, Kh

aleesat ta bi sa da kallo kafin ita ma ta bude motar ta sauka tana goge idonta, building din gidan taga ya nufa yana making phone call, ta bi bayansa tana tafiya a hankali, suna shiga parlon gidan bayan few minutes sai ga Hajiya Shafa'atu ta sauko downstai

rs ta karaso cikin parlon da fara'a tana masu sannu da zuwa Khaleesat ta zamo kasa daga kan kujera ta gaisheta cikin sanyin murya, Hajiya Shafa'atu ta

ɗ

agota ta zaunar da ita kan kujera kusa da ita tana amsa gaisuwarta da murmushi tace "Sannu da zuwa amary

a" Sai kuma ta kalli Ajay tace "Ni fa duk tunanina za ku yi few weeks kafin ku koma Amurka, ko dai za ku zauna Abuja ne for sometimes before traveling?" Ajay yace "A'a, Flight din na karfe sha dayan dare ne yau in sha Allah" Hajiya Shafa'atu tace "Ikon All

ah, yanxu baza ku jira ayi Walimar Jawwad da Hadiyah ba? It's taking place in few weeks time fa, Ina ga ya kamata ace kuna nan za ayi" Khaleesat dai sai kallon Hajiya Shafa'atu take babu ko kiftawa jin abinda tace, Ajay yace "She is resuming school this Mo

nday, kuma final semester ne" Hajiya Shafa'atu tace "Gaskiya kuma ya kamata ku koma saboda wannan, to Allah Ubangiji ya kai ku lafiya nima nan da few weeks za mu je Canada idan an gama Waliman an kawo amarya, kaga in mun koma ko weekend sai ka dinga kawota

tayi tunda daga Maryland zuwa Toronto ba nisa sosai garemu ba, Visa kawai zaka fara nema mata tun yanxu" Ajay yace "Haka ne" Wajen karfe uku suka isa garin Kano, Khaleesat taji ina ma ya kai ta gidansu taga Ummanta ko zata

ɗ

an samu relieve din abubuwan da

ke damunta suka tunkushe mata a rai, tun da yayi lodging dinta a wani babban hotel sannan aka kawo mata lafiyayyen lunch bata sake ganinsa ba har sai karfe shidda da rabi na yamma da yayi knocking, Bayan ta bude kofar yana kallonta a takaice yace "Where ar

e your Traveling document?" Khaleesat ta jingina da kofa tana kallon different direction kamar bazata ce komai ba sai kuma tace "Gidanmu" Yace "And you were quiet all this while, da hancinki zaki koma US din ashe" Ta wani kallesa tace "To ai ba a tambayeni

ba, don har nayi zaton an fara tafiya haka ne babu document" Yace "I will give you a dirty slap, ni kike gaya ma haka?" Tura baki tayi ta juya ta bar wajen ta koma cikin dakin ta zauna gefen gado ta rungume hannunta, kullo kofar dakin taga yayi, ta harari

kofar, tana ta baza ido ya dawo yace mata ta fito su tafi can gidan nasu ta dauko document din ko ba komai dai zata ga Umma amma shiru shiru bata ga ya dawo ba, sai karfe takwas saura ya dawo dakin yace "If you feel like leaving sai ki taso ki bar masu da

kinsu" Da ido ta bi sa har ya fita sannan ta ta

ɓ

e baki ta mike ta bi bayansa, yana zaune gaban mota sai drivern da zai kai su airport wanda dama shi yayi driving dinsu daga Bauchi, tana bude back seat ta shiga taga traveling document din nata a kan kujera

har da wayarta da Charger da ta bari a gida sanda za a kai ta Bauchi, lkci daya hawaye ya cika idonta ta daga kai tana kallonsa a gaban motar, shi ne bai tafi da ita gidan ba taga Ummanta, a haka suka bar hotel din tana jin hawaye na sauka idonta wani mugu

n haushinsa ya cika zuciyarta kuma bata fasa masa wani irin kallo ba wanda bai ma san tana yi ba a bayan motar.

*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah ur evidence via 07087865788*

Thanks so much for prayers and patience, I am better now

, nagode sosai.

HALYSAAH

PAGE 106

Khaleesat na zaune Departure lounge waiting for their flight to America bayan sun sauka garin Abuja, once a while take daga ido ta kalli Ajay da ke ta danna wayarsa don separately suka zauna far away from each other, gas

hi ko kallon inda take baya yi kamar ma ba tare suke ba, a hankali ta bude handbag dinta ta ciro wayarta dake kashe ta kunna, rabonta da wayar tun bayan da aka daura mata aure da abun duniya ya isheta ganin bata samun Jay a waya, bayan ta kunna taga tana d

a sauran caji, tasan har Safiyyah ta gaji da yi mata WhatsApp message, kilan in ta ji shiru tayi ma Aunty Farida magana, subscription ta fara yi kafin ta bude WhatsApp dinta, last message din da Sophie tayi mata ta bude tana dubawa taga tana ma online at t

he moment, hawaye ne ya cika idonta bayan ta karanta message din, kawai tace mata hm, message din na tafiya sai ga WhatsApp call Safiyyah ta doko mata, picking tayi ta kai kunne cikin sanyin murya tace "Sophie" Cikin farin ciki Safiyyah tace "Yau ni naga i

kon Allah wajen matar nan, daga yin aure sai kashe waya Coursemate?? wato don ma ki ci amarcin ki cikin lumana babu me takura ki da Housemate, shi dama angon is always not replying messages, wallahi nayi missing dinki sosai Khaleesat you won't understand,

yaushe za ku dawo plss, kinsan fa Monday za mu yi resuming" Khaleesat dake ta sauraron maganganun Safiyyah ta sauke idonta cikin sanyin murya tace "Yau za mu taso in sha Allah Sophie, nan da few minutes za mu yi boarding plane din" Safiyyah ta zaro ido wit

h excitement tace "Don Allah da gaske kike kawata, na zata fa sai nan da sati biyu za ku ce zaku dawo, toh Allah Ubangiji ya kawo min ku lafiya, har girki kuwa zan maku wallahi, i will even meet you people at the airport, Ina Housemate din? Plss ki ce ina

gaishesa sosai" Khaleesat ta kasa cewa komai, lokaci daya taji hawayen da ya taru idonta na zubowa, Safiyyah tace "Hello are you der?" Da kyar Khaleesat tace "Za mu yi boarding yanxu, bye" Safiyyah tace "Toh shkkn, pls in layover za ku yi ki min magana a k

asar da ku ka sauka, na ma san Layover ne, sai in san sanda za ku iso so that i will be at the airport" Cikin sanyin murya Khaleesat tace "Ohk, bye" Daga haka ta katse wayar ta mayar cikin jakarta ta daga kai tana kallon Ajay fuska daure. After some more m

inutes Khaleesat suka yi boarding jirgi and they were among the few first to board kasantuwar first class passengers ne su, sake kallon ticket dinta tayi da mamaki don duk tunaninta Business Class ne, this is her first time flying first class and it was st

range to her ganin luxury din, Duk da comfort and premium luxury na first class ita kam she wasn't comfortable bayan tashin su Abuja da few hours saboda Motion sickness da ya taso mata wanda bata fiye yi ba ma a jirgi sai ko in tana cikin damuwa, sau uku t

ana zuwa lavatory in taji amai ya taho mata, Flight attendant din was trying all possible best to see she is comfortable don da ta tafi zata dawo still to check on her and see if she's okay, sosai ta bata kulawa Flight attendant din, har daga karshe Khalee

sat tayi converting seat dinta into lie flat bed tace mata zata yi bacci sannan ta kwanta ta rufa har kanta da blanket, duk Ajay na kallonsu ko da ba kusa suke ba cause there is enough space separating them, bayan kusan awa daya Khaleesat taji an sauke bla

nket din da ta rufe har kanta da shi, bude ido tayi suka hada ido da shi, yana duke yana kallonta babu yabo babu fallasa yace "Are you okay?" Da hanci ta amsa masa sannan ta kara jan blanket dinta zuwa kafadanta ta juya masa baya ta rufe idonta, mikewa yay

i ya koma seat dinsa ya zauna, har jirgin su ya sauka London for stopover Ajay bai sake ce mata komai ba a jirgin. A cikin airport din ma ko kusa da inda take bai zauna ba suna jiran connecting flight dinsu to Baltimore, ita dai taki zama sai Safa da marwa

take a Departure Lounge, she looks so uncomfortable, lokaci lokaci take satan kallonsa duk da yaki ma kallon inda take kamar bai san Allah yayi ruwanta ba, can dai ta dake ta nufi inda yake zaune ta tsaya amma kuma taki kallonsa tana wasa da veil din jiki

nta, daga kai yayi ya kalleta dai dai sanda ta saci kallonsa, tana ganin sun hada ido ta

ɗ

an turo baki ta sauke idonta a hankali tace "I am having issues" Kallonta kawai yake jin abinda tace, Tayi kasa da murya tace "I need sanitary pad" Ajay ya dauke idon

sa yayi shiru kamar me nazarin abinda ta fada, after almost a minute ya daga kai ya sake kallonta yace "Do I look like a pad vendor?" Ita dai taki kallonsa har sannan kuma bata fasa wasa da gefen gyalenta ba, bai sake ce mata komai ba tsabar mamaki ya tall

abi chin dinsa yana girgiza kafa, can dai ya kuma kallonta yace "So as the lady you are you don't even know ur Cycle to prepare ahead?" Nan ma dai Khaleesat taki kallonsa taki cewa komai, Gyara zamansa yayi yace "Thank God is ur self you are going to disgr

ace here not me, nayi maki kama da me siyar da sanitary pad da zaki ce min you need sanitary pad, ko kuma amfani nake da sanitary pad?" Kamar zata yi kuka tace "Ni dai don Allah ka duba min kafin a fara boarding...." Jin yayi banza da ita kuma babu alamar

zai tanka mata don wayarsa ma ya hau dannawa, tana ta tsaye for almost 5 minutes a wajen, a hankali ta juya kawai ta bar kusa da shi ta koma can inda take tsaye ta ci gaba da tsayuwarta tana kallonsa, after some minutes ta ga ya mike, daya daga Lounge staf

f din dake wajen Ajay ya nufa for assistance or even a concierge service request if possible don bazai iya fita daga Departure lounge din just like that ba, not too long after sai ga shi an kawo masa sakon da ya bukata, tun da Khaleesat taga Ajay ya nufota

rike da ledan Sanitary pad tayi saurin dauke kai kamar bata san yana zuwa

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login