Showing 486001 words to 489000 words out of 641791 words
samari muke ma murmushi ba mazan aure ba" Tana kai wa nan ta mike tace "Bara in je in dawo" Khaleesat ta bi ta da kallo har ta fita, wayar Safiyyah ya fara ringing Khaleesat ta mike
zaune ta dau wayar taga Ajay ke kiranta, hade rai tayi ta ajiye wayar ta koma ta kwanta.... Safiyyah na fita kofar gidansu ta tarar da Jay tsaye jikin motarsa ya rungume hannu yana jiranta, har zata fara dariya ta tuna abinda Khaleesat tace mata, yace "Ash
e ba ku da nisa sosai da gidan frnd din nawa" Tace "Da gaske? Ina friend din?" Ya nuna mata cikin mota, abokin ya sakko ya zagayo suka gaisa da Safiyyah da fara'a sannan ya koma cikin mota, Safiyyah tace "To ya Kano Yaya Housemate?" Yace "Alhamdulillah, ya
mutanen gidan?" Tace "Lafıya lau wallahi, Mami tana lafiya?" Yace "Sure she is fine" Tace "To maa sha Allah, i so much appreciate the visit" Yace "You are welcome Safiyyah, zan koma.... Ki gaida mutanen gidan" Tace "Ohk but if babu damuwa ina son za mu yi
wata er magana da kai Yaya Jawwad" Yace "Ohk, am all ears Safiyyah" Tace "To bari mu zauna a compound cause it's confidential" Yace "Alright" Gate din gidansu ta nufa, ya kalli abokinsa yace masa yana zuwa sannan ya bi bayanta, kujeran dake compound din t
a dauko biyu ta ajiye masa daya, ita ma ta zauna kan daya, bayan ya zauna yace "Ina jin ki Safiyyah Safiyyah ta gyara mayafinta cikin nutsuwa tace "Dama magana ne akan Ajay da Khaleesat" Jay ya sauke idonsa bai ce komai ba, Safiyyah dai Kallonsa kawai take
, jin tayi shiru bata ci gaba ba, ya daga kai ya kalleta, sai kuma ya dan yi murmushi yace "Ina jin ki Safiyyah, what about them?" Safiyyah ta sauke ajiyar zuciya tace "They had issues" Jay yace "Issues? Wani irin issue kuma?" Safiyyah tace "As I am speaki
ng to you now Khaleesat tana gidan nan" Shiru Jay yayi wondering if ba su suka je can gidan jiya da daddare ba suka samesa, Can yace "I don't know the type of issue you are talking about" Safiyyah tace "Daxu ta zo, ta kuma gaya min duk abinda ya faru" Jay
ya gyara zama yace "Ohk, ai da sai kiyi abinda ya kamata kiyi masu without involving me Safiyyah, they trust you shi yasa har aka gaya maki, ke kuma sai ki gaya ma outsider sirrin su?" Safiyyah ta girgiza kai a hankali tace "Everything happen because of yo
u" Jay na kallonta da wani expression yace "I don't understand Safiyyah tace "Ajay ne wai yace mata zai saketa, saboda...." Katse ta Jay yayi yace "Kar yace saboda ni cause i won't take that likely, idan yana da niyyar sakinta to kar ya danganta hakan da n
i, I told him I hold no grudges against him and his marriage to saboda me zai ci gaba da fakewa da ni every now and then? He should stop involving me in his family matters pls, Ajay should stop painting me black and making me look like a demon" Safiyyah da
i kallonsa kawai take, sai kuma ta girgiza kai tace "But i wasn't expecting this from you Jawwad, na zata da na gaya maka zaka yi bringing an end to everything by speaking to them like the senior brother that you are, from the look of things Ajay meant his
words, yana ganin idan ya rabu da ita shi ne za ku dawo yanda kuke a da dashi, nasan damuwar yanda ku ka yi splitting ne yasa yayi wannan furucin cause he definitely cares about you so much kai ma kuma ka sani...." Jay yace "Safiyyah.... ya fada ne not be
cause zae iya aikatawa, ya fada ne don bakinsa yayi masa dadi, but kinsan me zai faru?" Ta girgiza masa kai tace "A'a" Yace "Zan kirasa inji yana ina, sannan idan za ayi permitting din ki a gida za mu je can tare, or you take an Uber to the House mu hadu a
can gaba daya, zan kuma sake maimaita abinda na fada masa kwanaki so you keep bearing me witness.. Safiyyah ta sauke ajiyar zuciya tace "Ai har da Khaleesat ya kamata duk mu je so that all this will end plss...." Jay yace "A'a babu ruwana da saka matar au
re a motata...." Murmushi kawai Safiyyah tayi tace "Ko kuma kasan yanda ya kamata mu yi?" Yace "Ina jin ki" Tace "Why not ni inyi magana da Ajay ince ya zo nan gidan, idan ya so sai mu zauna parlon baki ayi duk maganar da za ayi, ita ma Khaleesat zan sa ta
sauko zuwa parlon without telling her anything, shi ma Ajay din bazan nuna masa tana gidan nan ba, bazan kuma nuna masa kai ma kana nan ba, kawai cewa zan yi ya zo, wallahi ya Jawwad idan ba hadasu kayi ba kayi masu magana baza su taba samun rest of mind
din zaman aure ba more especially Ajay, amma idan kayi masu magana as the elder brother that you are ka hada masu da nasiha nan za su tabbatar da gaske babu komai a ranka, and they will leave comfortably as married couple" Jay ya dan yi murmushi yace "Yanx
un ance maki they are not leaving comfortably ne...." Safiyyah ma dai tayi murmushi tace "Ni dai plss do this Ya Jawwad" Ya daga ido ya kalleta ta marairaice tace "Don Allah, do this Yaya Housemate" After few seconds yace "Alright, you can call him Safiyya
h" Tace "Kai amma naji dadi kuma Nagode for doing this to me Ya Jawwad, bari in dauko wayata...." Mikewa tayi ya bi ta da kallo yana tunanin if he can truly do this, ya lumshe ido ya girgiza kai, sai kuma ya dafe kan na kusan minti daya, can ya sauke wani
boyayyen ajiyar zuciya ya mike ya fita daga compound din ya koma cikin motarsa, ya tada motar yana kallon abokinsa yace "Mu je za mu dawo anjima" It didn't take Safiyyah long to convince Ajay to come over to her parent House, don ta lura ido rufe yake nema
n Khaleesat, yana isowa gidan ta tafi har visitor parlor da shi, ya zauna kan kujera yana kallonta da damuwa yace "Don Allah tana nan ne Safiyyah?" Safiyyah na kallonsa ganin duk a daburce yake tace "You need to calm down Yaya Junaid Jingina yayi da kujera
n da yake zaune trying to calm himself down kamar yanda ta fada, tace "Ina zuwa" Daga haka ta fita daga parlon, Jay da ya dawo unguwan this time around shi kadai ba tare da abokinsa ba, shi ma tayi masa iso har zuwa visitor parlor din, sau daya ya kalli Aj
ay ya tafi ya zauna kan kujera, Ajay ya daga kai ya kalli Safiyyah da ta langwabar da kai tana dan murmushi, sai kuma tace "Ina zuwa...." Fita tayi daga parlon, Ajay ya dan kalli Jay suka hada ido, Jay yace "Sannu da aiki.... Safiyyah na komawa sama ta dau
ko ma Khaleesat gyalenta bayan tace ta zo downstairs su gaisa da babanta ya dawo, Khaleesat ta mike zaune da kyar tace "Wallahi ina jin kamar jiri Sophie, I don't know ko zan iya sauka downstairs" Safiyyah tace "Zaki iya, kawai dai ku gaisa ne fa ki dawo k
i kwanta" Khaleesat ta daure ta sauka daga kan gadon, Safiyyah ta rike hannunta suka fita daga dakin, a haka suka sauka downstairs ta tafi da ita har visitor parlor, tun Khaleesat bata karasa shiga parlon ba taji kanta na juya mata saboda kamshin turaren d
a parlon yake, banda Safiyyah tayi saurin rikota da tuni ta fadi kasa, Ajay bai san sanda ya mike da sauri ba ganin zata fadi, and he immediately sat down back bayan ya tuna Jay na parlon, Khaleesat ta kalli Safiyyah sannan ta kalli wa enda ta gani zaune p
arlon, lokaci daya ta fixge hannunta daga na Safiyyah a fusace tace "Meye haka kika min Safiyyah? Safiyyah tace "Mu je ki zauna" Cikin fushi sosai Khaleesat ta fashe da kuka tace "Bazan zauna ba wallahi, kuma idan na maki Allah ya isa sai ya bi ki, ba dai
saki na yace zai yi ba, ai sai ya sakeni tunda ya fadi haka don bazan sake zama da shi ba, na gama zama da shi har abada, yaje can ya zauna da dan uwansa da yace yafi ni, ai nima ba ni nace a aura min shi ba balle yace dan uwansa yafi ni, sannan he is dece
iving his self idan yana tunanin in ya sakeni zan yarda in auri dan uwan nasa kamar yanda yace, this is the least thing I will do in this life, iyayena ba gantalallu bane haka nima, kuma bana son ganinsu gaba daya...." Tana kai wa nan ta fice daga parlon t
ana kuka sosai.
HALYSAAH PAGE 164...
Jay ya juya ya kalli Ajay da ya bi Khaleesat da kallo looking so confused and lost, ba karamin nesa ya kai zuciyarsa ba na ganin bai tashi ya bi ta ba, a hankali ya mayar da kansa jikin kujera yana jin zuciyarsa na w
ani irin bugawa, calmly Jay yace "Junaid.... you are making it look as if ni ne genesis din rashin zaman lafiya a rayuwar aurenka, tell me why you are doing this to me? Ta yaya zaka dinga danganta issues dinka da ni??" Safiyyah ta karasa cikin parlon tace
"No No Ya Jawwad, all this talk isn't necessary now, duk babu amfanin wannan maganar a yanxu, didn't you miss the beautiful bond you once share with ur brother? Why did that bond disappear just like that piss Jay yace "You should be asking him that Ajay ya
wani kallesa amma yaki cewa komai, Safiyyah ta zauna tace "Don Allah ku zauna ku tuna good times dinku na baya sannan ku duba what is happening now, me yasa za ku bari shaidan yayi succeeding a kanku, why pause ur bond that's so beautiful to watch?" Jay y
a kalli Safiyyah yace "Zan samu takarda da Biro wajen ki?" Safiyyah tace "Na me fa?" Yace "In dai za a samu ki bani Mikewa tayi ta nufi Shelf din dake Parlon na litattafai ta dubo takarda da pen sannan ta dauko ta tafi ta mika ma Jay ya amsa sai kuma taga
ya mike, ita dai kallonsa kawai take, taga ya nufi gun Ajay, kallo daya Ajay yayi masa ya sauke Idonsa, Jay ya karasa har gabansa ya tsaya sannan ya mika masa takarda da Biron yana kallonsa yace "Tunda kace na fi ta a wajenka gashi nan ka sallameta sai mu
dawo yanda muke if that is ur only problem now" Safiyyah ta bude ido sosai tana kallon Jay da mamaki, Ajay ma ya dinga kallonsa babu ko kiftawa kamar yanda Jay din ke kallonsa shi ma, Safiyyah ta karasa kusa da su da wani expression tace "What's this u are
doing Yaya Jawwad? Ban gane ba" Jay ya kalleta yace "Don in tabbatar ko he meant all his words or he is just sugar coating, ya sallameta sai mu dawo yanda muke a da, i also miss him.... Safiyyah bata san sanda tayi masa wani kallo ba tace "Ban gane ba? Ya
sallameta kamar yaya? Meye kake fada haka??" Ajay ya sauke idonsa a hankali, sai kuma ya mika hannun ya amshi takardan da Biro, yana daura pen din a takardan kusan a tare Jay da Safiyyah suka kai hannu za su karbe pen din, Jay ya rigata amsa yana kallon A
jay calmly yana wani murmushi yace "Zaka rubuta i am sorry i can't bro ko?" Ajay ya mike yana masa wani kallo yace "Zan dai yi abinda kace since that is wat you want, sai ka koma ka gaya ma Mai martaba abinda ka sa nayi cause i am not going back to Bauchi
forever from here" Turasa Jay yayi har sai da ya fada kan kujera yace "Raina ma kanka hankali dai Junaid, in ma bindiga aka sa maka kayi haka ba sai dai a harbe ka ba Daga haka ya bar wajen ya koma ya zauna kan kujera, shirun few seconds ne ya biyo baya a
parlon, a hankali Jay yace "Okay let me say saboda a banza ka sameta babu wani stress babu wani damuwa shi yasa kake furta zaka saketa now and then, assuming you suffered before getting her ko wani ne yace ka saketa ka dena kulasa kenan har duniya ta tashi
koda da wasa ya gaya maka haka, did u even know the value of ur wife da kake ikirarin sakinta every now and then? To please who? You mean me?" Murmushi Safiyyah tayi ganin bad look din da Ajay ke yi ma Jay baya ko kiftawa, Jay ya kalli Safiyyah yace "Call
your friend Safiyyah" Safiyyah ta sauke ajiyar zuciya tace "Kasan bazata yarda ta biyo ni ba kuma yanxu ae" a hankali Jay yace "Ki gaya mata ni nace ta zo Safiyyah tace "Alright" Juyawa tayi ta bar parlon, ta tafi can sama zuwa dakinta, kwance taga Khalee
sat a gefen gado tana share hawayen dake ta zuba idonta, Safiyyah ta zauna kusa da ita tace "Kiyi hakuri kawata, kinsan bazan yi duk wani abu da zai cutar da ke ba, i only did what a friend is suppose to do... Khaleesat ta mike zaune tana kuka tace "Ni wal
lahi cutar da ni kika yi Sophie, na ce maki ina son ganinsu ne? Me yasa za ki min haka gashi ina jin wani irin bacin rai yanxu, i trust you shi yasa fa na zo nan amma kika min haka" Safiyyah tayi kasa da murya tace "Pls calm down Khaleesat, kinsan baki jin
dadi, kiyi hakuri ki dena wannan kukan, yanxu ki daure ki tashi mu je Jay yana kiranki Khaleesat ta watsa mata wani kallo tace "Babu inda zan je tana fadin haka ta koma ta kwanta fuskarta a murtuke, Safiyyah ta dinga kallonta babu ko kiftawa, can tace "Am
ma ban za ci zaki ce haka ba, don Jay kam ya wuce duk yanda kike tsammani a rayuwarki, idan kin daukesa da mutunci bai kamata kice baza ki je kiransa ba, Jay yafi karfın haka a wajenki wallahi, i tot you will see him as a senior bro da ya isa dake, ko dai
kin mance wanene Jay ne a rayuwarki Khaleesat?" Kuka Khaleesat ta fara yi a hankali, Safiyyah tace "Kiyi hakuri ki tashi mu je" Cikin kuka Khaleesat tace "Amma ni bana son ganin Junaid, idan ma yana nan ki ce masa ya tafı kawai ba a son ganinsa, zan je kir
an Ya Jawwad but Junaid shouldn't be there" Safiyyah tace "Ya ma tafi ai" Da kyar Khaleesat ta mike tana goge hawayen idonta Safiyyah ta dauko mata wani veil din don duk ta bata nata da hawaye, Safiyyah na rike da hannunta suka fita daga dakin suka sauka d
ownstairs, tsabar bacin rai Khaleesat har ta daina jin jirin da take ji, a haka suka isa visitor parlon din, suna shiga Khaleesat ta hada ido da Ajay, ta wani kalli Safiyyah har ta juya a fusace taji Jay yace "Halysaah" Sai ta tsaya taki juyowa wasu hawaye
n na zuba idonta tana jin zafi a ranta, Jay yace "Shigo ki zauna Halysaah" Ta juyo babu musu tana tafiya a hankali tana goge idonta ta tafi ta zauna kan kujera, Safiyyah ta juya zata bar parlon Jay yace "Ina kuma zaki Hajiya, get sitted too" Er dariya tayi
ta dawo ta zauna gefen Khaleesat dake goge hawayen da yaki tsaya mata, shi dai Ajay kansa na kasa ya ma kasa kallon Khaleesat, Jay na kallonta calmly yace "Bakin ciki kike saboda mijinki yace me first before his wife? Are you jealous of the bond?" Khalees
at ta daga kai ta kallesa taga murmushi yake, ta wani kauda kai, Jay was still smiling yace "Ikon Allah, to ba tare kika gan mu ba? Ko kuma bola kike son ya kai ni?" Nan ma dai Khaleesat taki cewa komai, Jay yace "A takaice dai idan ba mu bi a sannu ba rab
amu zaki yi kenan saboda kishin bond din mu, you just want to have him all to ur self? Do you have another brother for me sai in bar maki shi kawai?" Safiyyah dai murmushi kawai take, Jay ya dan kalli Alav vace "Since she is iealous of the brotherly bond,
gwara kace mata ka fi sona akanta da kace na fita a wajenka da duk ba a kai ga haka ba, i think this should be understandable." Safiyyah tayi dariya tace "So what's the difference between the sentence?" Jay yace "A'a kamar zata fi fahimtar wannan akan na f
arkon Khaleesat ta kalli Jay a hankali tace "Zan je in sha ruwa Safiyyah ta kalleta tace "Bari in kawo maki" Khaleesat ta mike da sauri tace "A'a i will get it my self Wani tashi take jin zuciyarta ke yi as a result of kamshin da parlon yake, sannan ko kay
an Ajay bata son ganin balle shi, his presence is only provoking her the more, Jay yace "To je ki dawo...." Ta gyada masa kai ta nufi kofa, da ido Ajay ya bi ta har ta fita daga parlon, Jay ya kalli Ajay authoritatively yace "Kai... You are to apologize to
ur wife for hurting her Ajay ya kallesa, kamar bazai ce komai ba sai kuma yace "Command on top 3 months seniority, not even up to 3 months cause June has 30 days, you've got to request and not command" Safiyyah ta zaro ido tana kallon Ajay trying hard not
to laugh, Jay ya gyara zama yana kallonsa shi ma, can ya dan yi murmushi ya mike ya kalli Safiyyah yace "Tashi mu tafi, a bar