Showing 531001 words to 534000 words out of 641791 words

Chapter 178 - HALYSAAH COMPLETE

hannunta na karkarwa tace "Wace Paridar?" Malam Ali ya

ce "Farida dai da kika sani" Nenne na gwalo ido tace "Wai Paridah Kanwar Zahra'u matar ka?" Malam Ali yace "Kwarai kuwa" Nenne ta fashe da kuka tace "Allahu Akbar, wai kana nufin sarki da kansa ko kuma dai wani yake nema ma aurenta?" Malam Ali yace "Cewa f

a yayi zai turo a daura masa aure da ita gobe, kuma ki ce wani Nenne, shi ne zai aureta, baki ga kai tsaye kawai har ya yanke gobe a matsayin ranan daurin auren ba babu wani dogon magana, ai Sarautar kenan, kuma bamu isa mu ce a'a ba...." Nenne ta gwalo id

o tace "Ka ji Malam Ali da wata magana kamar wawa, dama uban waye zai ce a'a? Ai babu shegen dake ja da maganar sarki" Nenne bata sake sauraronsa ba ta fice daga dakin da sauri ta tafi dakin Umma tana kwalo mata kira, Umma na zaune dakinta da Aunty Farida

har ta mike zata fita sai ga Nenne ta shigo kamar an jefota, sai kuma ta fashe da matsanancin kuka wanda Umma sai da ta tsorata duk tunaninta abu ne ya samu Khaleesat, Aunty Farida ma ta mike cikin tashin hankali tace "Lafiya Nenne, me ya faru?" Nenne ta d

uka ta dafe gwiwowinta cikin kuka tace "Wallahi Sarki ne da kansa ya kira Malam Ali yanxun nan" Nenne na fadin haka Umma ta fashe da kuka cikin tashin hankali tace "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un, me ya samu Khaleesat din Nenne? Ita ma mutuwan tayi?" I

ta kanta Aunty Farida jikinta rawa yake tsabar rikicewa tace "Abu ne ya samu Khaleesat din Nenne?" Nenne ta mike tace "Wacece Khaleesat kuma?"

HALYSAAH

Khaleesat na zaune parlon Mami da Dr dinta wajen karfe goma saura na safe, tagumi tayi tana kallon

akwatin ta da Dr Maryam ta zabar mata kaya kala uku da zata je Abuja da shi don ranan lahadi Mami tace za su juyo, Hadiyah ce ta shigo parlon da trolley dinta karami, Dr Maryam na kallonta tace "Da ke za ayi tafiyan Hajiyah Hadiyah?" Hadiyah tayi murmushi

tace "Inteesar ai kawata ce, mun yi Junior school tare lokacin muna Abuja kafin mu koma Lagos" Dr Maryam tace "Allah sarki, gaskiya kam ya kamata ki je" Mami ta fito daga dakinta cikin shiri ita ma, mai aikinta dake tsaye a parlon ta maza ta tafi ta amshi

akwatin ta, Hadiyah tace "Mami ba kince jirgin karfe sha daya bane" Mami tace "To ina ma naga me kai mu airport din, na kirasa bai daga ba ko yana can yana bacci, kawai bari ayi ma driver magana...." Dai dai nan Jay ya bude kofar parlon, yayi tsaye bakin k

ofar yace "Kun shirya Mami?" Tace "Kai nake jira tun daxu" Yace "To ku fito" Daga haka ya juya ya bar bakin kofar, Mami na kallon Khaleesat da tayi nisa tunanin da take tace "Tashi mu je Halysaah" Sai a sannan Khaleesat ta daga kanta ta mike a hankali tana

kallon Mami, Dr Maryam ta mike ta dau akwatin ta sannan suka nufi kofar fita parlon tare da Hadiyah da mai aikin Mami dake biye da su da akwatin Mami da na Hadiyah. Sai da Mami ta fara shiga wajensu Kilishi da Hajiya A'isha tayi masu sallama, Kilishi na t

sokanar Khaleesat wai sai kace ita ce amaryar sai sheki take, Khaleesat that was standing absently a wajen ta

ɗ

an yi murmushi, ita da babu abinda ta shafa a fuskarta, a haka suka fito compound suka tarar da Jay cikin motarsa yana jiran su, wani dogari ya b

ude ma Mami back seat da sauri yana jera mata kirari, Mami na kallon Khaleesat tace "Shiga Halysaah" Khaleesat ta shiga motar sannan Mami ta shiga dogarin ya kulle motar, Hadiyah ta zaga zuwa daya side din motar don wani dogari ya bude mata kofa ta can, ta

madubi Jay ke kallonta bayan ta shiga motar, ko sanin yana yi bata yi ba, Dogarai biyu suka gama saka duk boxes dinsu a booth din motar suna masu Allah ya tsare hanya, Dr Maryam ma tayi masu Allah ya kiyaye hanya, Mami tace "Ameen Dr, idan mun dawo zan ki

ra ki, amma kin yi ma drivern da zai yi dropping din ki magana?" Dr Maryam tace "Eh na masa magana, so nake in ga tafiyar ku tukun, ranki shi dade duk magungunan ta suna cikin zip

ɗ

in farko na trolley dinta...." Mami tace "To ba damuwa Dr" Dr Maryam tace "

Amma sai an sa mata ido ranki shi dade idan ba haka ba bazata sha ba...." Mami tace "Kar ki ji komai Dr zata sha" A haka Jay ya ja motar suka bar haraban masarautar, the ride was silent, after driving for almost 30 mins Jay ya ciro wayarsa a aljihu jin shi

gowar message for the second time, kiris ya rage ya buge motar dake gabansa har sai da Mami tace "Innalillahi wa Inna Ilaihi raji'un, lafiya Jawwad?" Yayi saurin controlling motar ya gangara gefen titi, Mami da Khaleesat da Hadiyah sai kallonsa suke, Mami

ta dake tace "Me ya faru?" Bai bata amsa ba ya bude motar da sauri ya sauka yana rike da wayarsa yana kallo, Mami ta bi sa da kallon mamaki, ita ma ta bude motar ta sauka tana kallonsa tace "Jawwad" Yayi saurin daga kai ya kalleta in a state of confusion,

sai kuma yace "Waya zan yi Mami" Daga haka ya bar wajen, walking a little distance away from the car, Mami ta kasa dena kallonsa, she wasn't convince with what he just said, hakan yasa ta sake bin sa har inda ya tafi ya tsaya tace "Wai lafiyar ka kuwa Jaww

ad? Me ya faru?" Jay ya kalleta cikin wani yanayi yace "Mami debit alert na gani daga account din Ajay" Mami ta bude ido sosai tace "Debit alert kuma? Baka sauke sim din nasa daga wayarka bane har yanxu dama?" Ya girgiza kai da damuwa karara fuskarsa yace

"Ban cire ba Mami" Da mamaki Mami tace "To ko wani ya samu Atm card dinsa ne ya cira kudin?" Jay yace "His ATM card is with me Mami, babu abinda ya dauka daga hotel room dinsa on that very day" Mami was speechless, after some seconds tace "To debit din ha

r nawa ka gani?" Jay yace "500k" Mami tace "500k?? Then who is tampering with the account?" Jay ya girgiza kai looking so worried yace "I don't know" Mami tace "To ko bankin zaka je? A ina aka cire kudin?" Jay yace "Bari inyi dropping din ku, i will call s

omeone at the bank yayi min confirming...." Mami ta sauke ajiyar zuciya tace "To Allah ya kiyaye, amma dai ina ga gwara ka kira bank din yanxu kar a ci gaba da cire kudin?" Jay ya fuzar da iska yace "Bari in kai ku airport din tukun...." Juyawa Mami tayi t

a koma motar ya bi bayanta, Mami na shiga motar Khaleesat na kallonta tace "Mami me ya faru?" Mami ta

ɗ

an yi murmushi tace "Kiransa aka yi emergency daga asibiti" Khaleesat tayi shiru bata ce komai ba, Jay ya shiga driver seat ya ci gaba da driving din, ha

r ya kai airport baya tare da nutsuwar sa kwata kwata, a nan parking space din airport din ya bar su bayan ya fiddo masu da boxes din su daga cikin booth porters sun shiga da akwatunan cikin airport, Mami na kallonsa tace "Duk yanda ake ciki za mu yi magan

a" Jay ya gyada mata kai yayi masu Allah ya kiyaye sannan ya koma cikin mota ya ciro wayarsa yana kara kallon debit alert din, bude ido yayi sosai with another new shock bayan ya lura ashe an turo debit na sabon Atm card before the 500k debit alert, ya din

ga kallon alert din babu ko kiftawa, yaji komai ya tsaya masa cak na wasu seconds, it took him some time to recover, barin airport din yayi within few minutes yaji gwara ma yaje bank din da kansa ya samu friend din nasa don gaba daya ya rikice... Ajay na z

aune kan dakali a kusa da bank bayan sun fito yana sauke numfashi a hankali, Ozhi dake tsaye kansa sai sannu yake masa yana masa fifita da bugujejen rigar jikinsa, shi dai Ajay kansa na kasa sai nodding masa kai kawai yake, Ozhi ya tari wani me siyar da pu

re water ya amshi guda biyu ya mika ma Ajay daya yace "Ga ruwa nan ka sha, tafiya ne yayi yawa tun safe shi ne kake jin hajijiya, ka gaji sosai" Ajay ya amshi ruwan da kyar ya bude ya sha kadan, Ozhi ya amshi sauran ya zuba masa a kai ya shafa masa a fuska

, suna nan for more than 15 mins idon Ajay a lumshe and he was breathing slowly, tun daga sanda suka hau kwale kwale daga Abinsi zuwa Makurdi ya dawo wani iri, and he started feeling nauseated and sick, all of a sudden kansa yayi ta juya masa sosai ga wani

sanyi da ya dinga ji har sai da Ozhi ya rungumosa yana lulubesa da ƙatuwar rigar jikinsa, a wahale suka isa garin Makurdi, sai da suka yi kusan minti ashirin a bakin hanya karkashin wata bishiya sbda yanayin condition din Ajay, daga karshe kuma yayi karfi

n halin ce ma Ozhi zai iya su ci gaba da tafiya, nan suka fara neman banki, har dai suka samu abun hawan da ya kai su bankin, a cikin bank din ma cike da dauriya Ajay ya gama abinda ya kai sa, aka basa sabon Atm card, don ma anyi attending masa da wuri an

kuma basa attention saboda condition dinsa, duk wanda ya kallesa yasan bashi da lafiya sosai kuma zai tausaya masa cause he is looking pale, haka nan ya samu yayi withdrawing kudi bayan sun fito daga bank din, shine ya zauna kan dakalin dake kusa da Atm ma

chine din ya kasa tashi, after a while cikin karfin hali Ajay ya mike a hankali yana kallon Ozhi yace "Za mu iya tafiya yanxu" Ozhi yace "Ka yarda kana iya tafiyan ko de mu bari in ka huta sosai sosai?" Ajay ya gyada masa kai duk da karfin hali kawai yake,

Ozhi yace "To mu je" Yana fara tafiyar yaji he can't go further, ya kalli Ozhi yace "Ba wani hanya sai ta inda muka bi muka zo yanxu?" Ozhi yace "Kwale kwale ne kawai muke hawa zuwa village din mu, muyi sauri sauri mu tafi Dochu ya baka magani, ciwo kar y

a dawo kuma" Ajay ya gyada masa kai kawai ya ci gaba da bin sa, ko minti biyar basu yi suna tafiya ba vision dinsa ya koma blur, both motoci da mutanen da ke hada hadar su a wajajen ya dinga ganinsu double, lokaci daya ya fara ganin duhu duhu, dafa Ozhi ya

yi ya fara yin baya, tun kan ya kai ƙasa Ozhi yayi saurin rikesa da taimakon wasu dake bayansu, gefen hanya suka zaunar da shi amma he is already passed out, Ozhi ya cire ƙatuwar rigar jikinsa da sauri yana masa fifita, wani mutumi ya karbi pure water daya

ya bude yana yayyafa masa ruwan, wasu ne suka ce a tafi da shi asibiti kawai, Ozhi dai yayi saurin cire kudaden jikin Ajay ganin yanda aka taru kansa, haka nan aka daukesa zuwa asibitin dake nan wajajen, bayan

ɗ

an lokaci kowa ya watse aka bar Ozhi kadai a

reception din asibiti, ko kadan bai so asibiti da aka kawo Ajay ba, so yayi ya maida sa kauyensu a ci gaba da yi masa maganin sa, gashi sai mamakin kudin da Ajay ya ciro masu yawa a banki yake, wata nurse ta zo ta samesa a reception din tana sanar masa za

i ajiye dubu ashirin kudin deposit, Ozhi na zare ido yace "A'a bai ce a ta

ɓ

a masa kudinsa ba" Nurse din tace "To kuwa zai mutu tunda baza a ta

ɓ

a kudinsa ba, kudin nasa yafi rayuwarsa ne?" Ozhi yayi shiru, sai kuma ya ciro kudin a aljihunsa ya kirga dubu as

hirin ya ba Nurse din tace "Ai ba ni zaka ba ma ba, ga can inda ake biya kaje ka biya za su baka takarda" Wajen da ta nuna masa ya nufa da sauri zai kai kudin, har wajen karfe biyar na yamma Ozhi na ta zaune reception din asibitin sai gyangyadi yake yi, da

ga karshe wata nurse ta tashesa yaje office din likita yana son magana da shi, yana kankame da kudin Ajay dake jikinsa ya tafi office din da aka nuna masa, ya ga likitan na zaune yana ta rubuce rubuce a takarda, ganin Ozhi ya tsaya likitan ya nuna masa kuj

era alamar ya zauna sannan ya zauna, likitan yace "Wannan patient din

ɗ

an uwanka ne ko ya kuke da shi?" Ozhi ya gyara zama yace "Eh dan uwana ne, muna tare shekara biyu kenan amma ni ban san shi ba" Likitan ya daga kai ya kallesa, sai kuma yace "Ɗan uwanka

ne amma kuma baka san shi ba? Ban fahimce yaren ka ba" Ozhi yace "To ni dai

ɗ

an uwana ne amma ban san wanene shi ba" Likitan that was getting pissed off yace "A ina ka san sa?" Ozhi ya kara gyara zama ya fara basa labarin abinda ya hadasa da Ajay har zuwa

yau, likitan sai kallonsa yake babu ko kiftawa with much interest, can ya ajiye biro din hannunsa yace "Amma wanene ya cire masa bullet din jikinsa?" Ozhi yace "Native Dr din garinmu mana, Dochu sunansa" Likitan sai kallonsa yake, can yace "What if crimin

al ne shi, duk baku yi wannan tunanin ba?" Ozhi ya gyara zama yana girgiza kai with seriousness a maganarsa yace "Noo, ai wannan fuskarsa babu criminal, mutumin kirki ne, shi ba criminal ba" Likitan ya wani kallesa yace "Dama ana rubutawa a fuska? To kaga

irin wannan case din dole sai mun yi involving yan sanda to avoid problem, tunda baku san wanene shi ba, baku san dalilin da yasa aka yi harbinsa ba, baku kuma san dalilin harbin nasa ba, mu ma kuma bamu san sa ba, so we have to involve the police in this

case, har yanxu akwai fragments din bullets a jikinsa which has lead to some complications for him, yanxu dai kafin mu kara ta

ɓ

a sa sai an sanar ma yan sanda wannan case din" Ozhi yayi shiru yana kallon likitan, can yace "Zan gansa ne yanxu Doctor?" Dr din

yace "Yeah zaka iya ganinsa, mu je ka gansa" Mikewa Ozhi yayi ya bi bayan likitan zuwa ward din da Ajay yake, yana kwance idonsa a lumshe, although he is revived by the Doctors amma he was still weak, ciwon kansa ya karu akan na da duk da drip din da ake

kara masa ji yake kamar ana sara masa kansa, bai yarda ya bude ido ba yayi kamar bacci yake bayan ya ji sun shigo, Dr din na kallon Ozhi yace "Kafin mu kara ta

ɓ

asa sai idan yan sanda sun zo gaskiya, saboda ba a san wanene shi ba" Ozhi yace "To, to ai sai k

u kira su su zo, ni dai nasan mutum na kirki ne shi" Dr din ya juya ya fita daga ward din, sai a sannan Ajay ya bude ido a hankali, Ozhi yayi kasa da murya yana tsaye kusa da shi yace "Abokina ka tashi muyi gudu wa rayuwarmu, za su je su kira mana yan sand

a ne, ka tashi mu yi gudu mu koma village din mu Dochu yayi maka magani da yake maka, yan sandan garin nan babu kyau suna kashe mutane" Ajay yayi shiru yana kallon Ozhi, can yace "Ka fara siyo min ruwa na sha zan ji karfi sai mu tafi" Da sauri Ozhi ya ajiy

e kudaden hannunsa a gefen Ajay ya dau dubu daya a ciki sannan ya fita zai je nemo ruwa, Ajay ya laluba jikinsa yaji sabon Atm card din da yayi, kayansa ne a jikinsa don matar Ozhi ta wanke masa tayi stitching din inda bullet ya huda, ana ta ajiyar kayan t

un da dadewa, har sai yau da za su taho banki ta dauko masa ya saka su, a hankali Ajay ya mike zaune ya zare drip din hannunsa sannan ya sauka daga kan gadon ya dau kudaden ya saka a aljihu ya fita daga ward din, kansa tsaye with confidence ya nufi kofar d

a yaga alamar na fita daga reception ne without looking at anybody har ya fita, sai da ya fita ya fara tafiya da sauri har ya fice daga asibitin gaba daya ya tare adaidaita sahu ya shiga, ya jinginar da kansa da kujeran adaidata sahun yana sauke numfashi,

ɗ

an tafiyar nan da yayi jinsa yake kamar wanda ya yini yana gudu, he was so weak.... Mami na tafiya a hankali ta fito compound din gidan Ammi tana kallon Jay dake zaune kan kujera kusa da parking lot ya rike kansa, it was almost magrib time, tun karfe daya

na rana suka sauka garin Abuja, tun daga sannan kuma take ta kiransa baya daga waya har hankalinta ya tashi sosai, ta kirasa ya fi a kirga amma shiru, kawai gangar jikinta ne ke Abuja amma zuciyarta na can Bauchi, har Kilishi ta kira ta tambaya ko Jay ya

koma gida tace mata bai koma ba, and this almost caused her a heart attack kawai dauriya take tayi ga gida cike da yan biki, all of a sudden sai gashi yanxu ya kirata wai ya shigo gidan Ammi yana parking lot, duk da wani relieve da ya zo mata amma tayi mam

akin zuwan nasa Abuja all of a sudden don basu yi da

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login