Showing 498001 words to 501000 words out of 641791 words
komai ba can dai yace "I never said I need a new shirt, I have many of them in my box me yasa baka bude akwatin ka bada nawa ba, idan na shiga ciki zan cire maka in ba Dry Cleaner rigar.... Daga haka ya sauka daga motar sannan y
a juya yana kallon Jay yaga shi ma ya sauka daga cikin motar looking at a different direction. A main parlor Ajay ya zauna ya jingina da kujera ya lumshe ido, the house feel so empty without his wife, ji yake kamar sun yi shekara da shekaru tare da ita, ju
st jiya da ya kwana shi kadai babu ita by his side the night became so long and restless for him, don ko baccin kirki bai yi ba daren jiya. Da yarmma sosai Ajay ya fito daga bangarensa ya tafi part din Jay, a bakin kofa suka hadu Jay din zai fita, Ajay na
kallonsa yace "Zaka je gidan Hajja ne?" Jay yace "A'a" Ajay bai sake cewa komai ba ya nufi parlon sarki don tunda suka dawo bai je ya gaishesa ba cause yana da baki a lokacin, Mai martaba na zaune parlornsa da Aunty sai Walid, Aunty tayi kasa da murya tace
"Allah ya taimake ka, tunda har yayi deciding zai yi karatun yanxu kayi hakuri ka basa last chance, lokaci bai kure masa ba...." Dakatar da ita Mai martaba yayi yace "There is no last chance for Walid Fulani, asaran karshe da yasa nayi shi ne na biya masa
kudin makaranta a Oxford, bayan wannan asaran bazan kara wani ba, kasashe nawa na biya masa karatu da ya fara sai ya gudo ya dawo Nigeria? So babu zancen biya masa kudin karatu a wata kasar, ga Universities iri iri a Nigeria idan har da gaske karatun zai
yi ya zabi wanda yake so a ciki amma ba dai kasar waje ba" Aunty tayi shiru tana kallon Mai martaba tana jin zuciyarta na tafarfasa, Walid ya gyara zama yana kumbure kumbure yace "To ni kawai ranka shi dade a bani kudi inyi setting din business of my own,
ko da miliyan dari ne a bani kawai in ja jari inyi establishing business me kyau, in sha Allahu kuma sai kayi alfahari da business din" Mai martaba yace "Akwai sabon kamfanin da na bude a kasar Nijar, i am placing Jawwad and Junaid in charge of it, so idan
kamfanin ya fara aiki zaka dinga bin su zuwa kasar Nijar kana saka ido kana ganin yanda al'amuran kamfanin suke tafiya, idan naga you are serious and dedicated zan sa su sakar maka ragamar kamfanin, since they are already managing the one in Lagos, Jawwad
is also managing the one in Port Harcourt, so next week zan sa su je Nijar su duba ma'aikatan da aka dauka a kamfanin, all due process steps have being followed... aiki kawai za a fara, sai ka shirya ku tafi gaba daya da su Aunty sai kallon Mai martaba ta
ke ranta na kuna, kawai ya maida mata yaro mara gata mara galihu a gidan nan komai sai dai ya sa Jawwad, sanda ya ga dama kuma ya saka Junaid, amma Walid ko oho an maida mata shi dan iska mara future, Walid na sosa kansa yace "To Nijar a wani gari kamfanin
yake ur highness?" Mai martaba yace "Idan ku ka je zaka gani Dai dai nan Ajay ya shigo parlon da sallama, sauke kansa yayi ganin wa enda ke zaune parlon Mai martaba, da yasan suna ciki ma bazai shigo ba kawai tafiyarsa zai yi gidan Hajja, haka nan ya kara
sa cikin parlon ya zauna ya gaida Mai martaba da ladabi kansa a kasa, Sarki ya amsa, Ya daga kai ya gaida Aunty ta amsa tana kare masa kallo daga sama har kasa, Walid tuni ya hade rai ya kauda kai yana kallon wani direction daban a parlon, Aunty tace "Ina
Halysaar? Ashe kun dawo..." Kamar Ajay bazai yi magana ba, can yace "Mun dawo" Mai martaba yace "Ya baka taho da ita ba" Ajay yayi kasa da murya yace "Bata da lafiya ne ranka shi dade, shi ne na barta can gidansu a Kano" Da mamaki Aunty tace "Subhanallahi,
bata da lafiya tun yaushe?" Ajay yaki ce mata komai, Mai martaba yace "Me yasa zaka bar ta gidansu bata da lafiya baka dawo da ita gidan nan ba, baza a iya kula da ita a nan gidan bane sai can Kano? Ko ka mance she is our full responsibility now not her p
arents?" Ajay ya girgiza kai a hankali yace "A gafarce ni ranka shi dade, it is not something serious shi yasa ma har na bar ta a can, stress din tafiya ne, kuma kwana biyu kawai zata yi in je in daukota in sha Allah" Aunty tace "Ya dai fi, kaje ka daukota
don bamu gaza ba, ai abun kunya ne ma wannan ga masarautar nan, matarka bata da lafıya ka maidata gidansu, menene amfanin mu?" Mai martaba dai bai sake cewa komai ba a parlon, Walid yace "I want to excuse my self ur highness" Mai martaba ya kallesa yace "
Ba dan uwanka bane ya shigo parlon nan ka dauke kai Walid?" Walid ya sosa kai yace "To ai gani nayi kuna magana ne ranka shi dade" Sai kuma ya kalli Ajay yace "Barka da dawowa Yaya, fatan kun dawo lafiya" Ajay ya daga kai ya kallesa yace "Alhamdulillah, ho
w are you?" Walid yace "Alhamdulillah" After some minutes Ajay yayi excusing kansa ya fita daga parlon. Gidan Hajja Ajay ya tafi, ko da ya isa gidan har an idar da sallahn Magrib, ya tsaya kofar gida yayi sallah a masallaci sannan ya shiga cikin gidan, zau
ne ya sameta a parlonta ita da Jay, kallonsa kawai Ajay yake yi har ya karasa cikin parlon ya zauna Hajja na yi masa sannu da zuwa da fara'a, gaisheta yayi ta amsa tace "Ina matar taka?" Ya sauke idonsa yace "Tana gidansu" Hajja tace "Gidansu kuma?" Saboda
me ka bar ta a gidansu?" Mai aikin Hajja ce tayi sallama bakin kofa Hajja ta amsa, bata shigo parlon ba da ladabi tace "Hajiya an gama shirya abincin a dinning table" Hajja ta kalli Jay tace "To an shirya maka abincin Jawwad.... Mikewa Jay yayi, Hajja na
kallon Ajay tace "Ka je ku ci abincin sai ka dawo Ajay yace "A'a... am okay" Shi dai Jay ya fita daga parlon, Hajja tace "Yanxu Jawwad ke ce min tare ku ka dawo daga Kano daxu" Ajay yace "Eh" Hajja tace "To Alhamdulillah, ai haka ake so, Allah Ubangiji ya
kara hada min kanku, nayi farin cikin jin hakan sosai" Shi dai Junaid bai ce komai ba, Hajja tace "Ita kuma Jeeddahn me yasa ka bar ta a gidansu?" Ajay yace "Bata da lafiya ne" Da mamaki Hajja tace "Bata da lafiya? Kuma shi ne ka bar ta a gida kamar mun ga
za? Me ya sameta?" Ajay yayi shiru, Hajja tayi kasa da murya tace "Ko juna biyu gareta Ahmad?" Ajay ya daga kai ya kalleta still bai ce komai ba, wani murmushi Hajja tayi ta daga hannu biyu sama tace "Alhamdulillah, Allah nagode maka, nayi farin ciki da wa
nnan labarin me dadi, Alhamdulillah ya Allah, tun yaushe Ahmad?" Ajay ya sauke idonsa yace "Da muka dawo ne ta fara rashin lafıya" Hajja tace "Ikon Allah, to gobe gobe in sha Allahu zan aika aje a taho min da ita, mu bama haka a gidan sarauta, a dawo da it
a kawai a masarauta zata zauna tayi laulayinta.
HALYSAAH
PAGE 168..
.
*This page is dedicated to one and only Rukky Bjw
🥰😍
ita din kanwar uwar Ajay ce me damuwa da duk wani abu da ya damesa, ita din me tayasa kukan maraicinsa ce
😁
shi kansa Ajayn ma y
a san da zamanki a duniyar Halysaah, i hail you with respect Sis Rukky yan Ethiopia, Allah ya albarkaci zuri'ar ki*
😍
Ajay yace "A bar ta dai Kanon tayi kwana biyu tukun Hajja" Hajja tace "Sam hakan ba me yiwuwa bane, dama yanxu Jawwad ke ce min uwarsa
na kano, zuwa anjima zan sa ayi min kiran Mai martaba in ce ya kirata ya sanar mata taje gidansu Jiddah ta daukota ta dawo da ita masarauta tayi jinyar jinjirin cikin jikinta, idan ya so daga nan sai a tura Hajiya Sumayyah ta tafi Kanon ta sameta su je gi
dan iyayen Jiddan tare su taho da ita" Ajay yace "To ai bata da lafiyan da zata iya bin hanya yanxu" Nenne tace "Babu jirgi ne daga kanon zuwa Bauchi? Idan ma ba a samu jirgi ba su bi jirgin Abuja kawai, daga Abujan su biyo jirgin da zai dawo garin nan ba
shikenan ba" Ajay dai kallonta kawai yake, tace "Ai da kayi shawara da mu bazaka fara barin ta a gida wai don bata da lafiya ba, haka kawai baza ka yanke hukunci kanka tsaye kamar baka da mafada ba, balle a irin babban gidan nan da komai ke da ka'ida kuma
bama wasa da al'ada, you are making it look as though we are not capable of looking after her, this is big slap to the Emirate as a whole" Ajay bai sake ce mata komai ba, kamar tasan tunanin dake ransa tace "Idan ma kana fargaban zamanta gidan sarki ne sai
a sauketa a nan ga dakuna nan sai wanda na zaba za a ajiyeta, za kuma ta zauna babu takura, sannan ga masu aiki da za su kula da ita kwarai da gaske, nima kuma zan saka mata ido sosai...." Ajay felt that is okay for him, amma bai san yanda za a kwashe da
Nenne ba tunda ta nemi alfarman ya bar masu Khaleesat har ta ji sauki ya kuma amince mata, yanxu kuma gashi za a aika daga masarauta aje a daukota, Hajja tace "Kayi shiru? Ko tsarin nawa bai maka bane kafi son a bar ta can masarauta?" Ya daga ido ya kallet
a yace "Bai fi tayi sati biyu fa a Kanon, bayan sati biyun ba sai aje a taho da ita ba" Hajja ta hade rai tace "To bamu lamunta da hakan ba, kuma bamu amince ba, zan je har gidan sarki da kaina in sanar masa ya aika mutane su je su taho da ita, yaushe aka
haifeka da har zaka canza mana tsarin gidan sarauta?" Ajay ya ta
ɓ
e baki ya mike ya koma kan kujera yace "To ki je ki daukota da kanki mana" Hajja zata yi magana Hadiyah ta shigo parlon da sallama, sai baza kamshi take ga make up ta sha a fuska, cire gyalen
ta tayi da takalma, ta jefa jakan hannunta kan kujera tana yatsine fuska tace "Shegen driver din nan kullum idan na fita sai na dinga kiransa ya zo ya daukeni kamar bai san aikinsa ba, dama amfaninsa ba ya zauna ya jirani ko awa nawa zan yi ba ya dauko ni?
Gaskiya canza min shi za ayi bazan iya surutu ba" Hajja na kallonta tace "Na dai raba ki da fita ki kai dare haka da aurenki Hadiyah, me yasa baki jin maganata ne? Kuma kina ganin kirana kika ki dauka" Hadiyah ta
ɗ
an kalli Ajay, da kamar bazata ce komai b
a sai kuma kamar dole tace "Ina wuni" Ba tare da ya kalleta ba a takaice yace "Lafiya" Fita tayi daga parlon zata tafi dakinta, Ajay ya kalli Hajja yace "Yanxu da auren kike bari tana fita har ta kai dare Hajja?" Hajja tayi kasa da murya tace "To ya zan ma
ta tunda tana son fita Junaid? kuma naga babu inda take zuwa sai wajen cousin sisters dinta sai wasu kawayenta dake garin nan, ai ba nisa take yi ba, kuma kai fisabilillahi baza ka ma
ɗ
an uwanka magana ya ajiye wannan tsinannen fushin nasa ba yarinyar nan
ta koma dakinta haka nan, duk an zuba masa ido an rasa me yi masa magana a kaf masarauta, yan uba sai murna da hakan suke tunda ba wai suna son ci gaban mu bane, ni sai naga ma kamar sarki tsoron Jawwad yake, to banda haka na ce yayi masa magana ya kai sau
uku sai dai Sarki yace za ayi masa abu ya doshi sati uku yanxu, shi yanxu Mai martaba yafi son yanda Hadiyar ke zaune gabana kenan? wannan abun kunya har ina?" Ajay yace "Ke me ya hanaki yi ma Jawwad din magana?" Hajja tace "Sau nawa kuma? Na masa magana
yayi sau goma in ma bai fi ba, har kiransa nayi a waya wallahi, yanxu ma da yaya na samu ya taho gidan nan? Tun safe nake kiransa ya baro Kanon nan ina son ganinsa, Ni ban ma san kuna tare a Kanon ba, wajen karfe biyar na sake kiransa daxu bayan kun dawo s
ai ce min yayi shi ya gaji bazai iya zuwa ba, na cire rai kawai sai gashi kamar an jefosa, tuni nayi ta kiran yarinyar nan ta dawo kar yaga bata nan amma taki daga wayata, ya shigo kenan sai ga ka" Ajay yace "Ni dai nasan daga ke har ita sai Allah ya kama
ku, tunda da aurenta kike supporting dinta ta fita gantali har da kai wa dare" Hajja ta hade rai tana kallonsa tace "Ni kake gaya ma wannan magana Junaid?" Ya mike yace "Ai ke dama baki son gaskiya, hanyar gaskiya daban hanyar da kika bi daban, yarinya na
misbehaving har yanxu shi ne ake son ta koma dakinta ba a dau hanyar seta mata zama ba" Hajja tace "Kaga fita ka ban waje kar raina ya
ɓ
aci Junaid, uwar me tayi da za a seta mata zama, akwai macen da take perfect dari bisa dari a dakinta ne dama?" Ajay yac
e "Oho dai, zaman da take a gida ne bai isheku ba shi yasa kike ganin she is not suppose to be perfect...." Yana kai wa nan ya fice daga parlon, Hajja tace "Munafukan banza kawai, dama ai duk bakin ku daya kai da Jawwad din gantalallu, kuma idan Jawwad baz
ai dena wannan kuturun zuciyar ba zai yi ta samun matsala ne a rayuwarsa, a haka za a basa rikon masarauta mutum baya kauda kai akan abubuwa komai sai ya hau dokin fushi, kai ba gashi kana zaune da matarka lafiya ba babu me jin kanku duk shakiyancin da ta
dinga yi maka bayan aure me yasa baka korata gidansu ba ita da take ba er kowa ba ma, akan idona na sha ganin yanda take nuna kai ba zabinta bane tana wasu abubuwa marasa kan gado amma haka ka hakura baka ta
ɓ
a kai ma kowa kararta ba...." Mikewa Hajja tayi
ta fita zuwa Main parlor cikin
ɓ
acin rai, tana kallon Jay dake zaune dinning tace "Dama ashe zuga ka ake shi yasa ka bar min yarinya kamar wata mara galihu a gabana har yanxu?" Ajay dai na zaune parlon yana kallon TV bayan yayi changing channel zuwa na foo
tball, Jay yaki ce ma Hajja komai, sai ga Hadiyah ta shigo parlon tana wani yatsine yatsine tace "Da galihuna wallahi Hajja, kar ma kice an bar ni a nan kamar mara galihu, da gatana kaca kaca, banda kaddara ma ni me zai sa in auri wanda uwarsa ke controlli
ng duk abinda zai yi a gidansa, hatta kudinsa ita ke controlling kamar wani karamin yaro, shi yasa ake kin biya min bukata ta...." Jay ya daga kai ya kalleta yace "Kee, Watch ur tongue" Ta masa wani kallon banza tace "To karya nayi? Ba baabarka bace ke con
trolling din ka? Ko zaka hanani fadin gaskiya ne, da ta hanaka zama da ni ai sai ta jika ka ta shanye mu ga" Mikewa yayi yace "To ki je na sake ki, sannan duk wani abu da yake naki a bangarena ku kwashe su kar in sa a fitar min da su" Daga haka ya figi way
oyinsa ya nufi hanyar fita daga parlon, ba Hajja da Hadiyah ba har Ajay dake zaune parlon sai da yayi shock, Hajja ta fashe da kuka jiki na rawa tace "Ko dai Jawwad ya fara hauka ne? Ko dai shaye shaye yake? Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un, me ya samu J
awwad haka" Ajay ya mike ya bi bayansa yana kiran sa, har ya isa compound Ajay ya cim masa, ya fixgosa yace "Are you on ur right senses Jay? Sakinta fa kayi?" Jay yace "Eh sakinta nayi, in kuma zaka hada da ita ne ga ka ga ta ai...." Ajay ya dinga kallonsa
babu ko kiftawa, barin sa yayi wajen a tsaye ya nufi motarsa ya shiga within seconds yayi zoom off daga gidan. Wajen karfe goma da rabi na dare Ajay na zaune parlon Mai martaba ta dalilin kiransa da Sarki yayi, shi kadai ne zaune parlon yana jiran fitowar
sarki daga parlornsa na ciki, Jay ne ya shigo parlon suna hada ido da Ajay ya sauke idonsa har ya karaso cikin parlon ya zauna, shi dai Ajay inda yake kallo daban a parlon, after some minutes Jay yace "I apologize for my outburst earlier this night Junaid
" Without looking at him Ajay yace "It's fine" Babu wanda ya sake cewa komai a parlon sai ga Sarki ya fito, kusan a tare suka mike, har ya karaso cikin parlon ya zauna sannan suka zauna, Ajay ya fara yi masa barka da dare sannan Jay ma yayi haka, Sarki ya
amsa, after a while yace "Akwai abinda ke damunka ne Jawwad that you are not telling us? Tell me what ur problem is" Jay ya sauke kansa kasa a hankali yace "Allah ya huci zuciyar Mai martaba, babu abinda yake damuna, a gafarce ni...." Sarki yayi shiru yana
kallonsa, can ya sauke boyayyen