Showing 618001 words to 621000 words out of 641791 words

Chapter 207 - HALYSAAH COMPLETE

03 Sep 2026

141

is, kin san halinsa, kuma har muka gama rayuwar Maryland baki ta

ɓ

a ganinsa da mace a sunan suna hira ba ko suna soyayya, sai dai ko abokiyar karatu kuma basa wuce turawa don baya ma harka da bakaken fat

a, so why are you being in secured now? Baki yarda da mijin ki ba kike nufi kenan? Ko kin kama sa da wani act ne mara kyau da ya sa kika zama not secured with him? Bai kamata kina

ɗ

aga masa hankali ba after all the challenges he faced in life, baki tunanin

wannan matsalar da ku ke samu now and then zai iya ja masa shiga wata damuwar daban? Ba fa yayi recovering fully bane daga abinda ya samesa Khaleesat, duka duka watanni nawa kenan da dawowarsa har za ki fara saka shi cikin damuwa? Ni wallahi na zata in th

e next 2 years to come za kiyi ta lallaba mijin ki ne ko bata maki rai yayi zaki shanye considering all what he went through for 2 years, meye don kawai warce ba musulma ba ta rungumesa, su ai a wajensu ba komai bane hakan da tayi, she was just happy to se

e him, shi kuma kinga ai bazai gwaleta ba duba da hidimar da suka yi da shi, kuma mutanen nan dai ya kamata su zama second family din ku, don da ba don su ba da wani zance muke yanxu ba wannan ba, Ajay is alive today as a result of their help Khaleesat, ki

ka san gwagwarmayar da suka sha wajen nema masa traditional medicine da har ya farfado? Kika san effort dinsu akan Ajay? Duk wanda zai maka haka ai ba abun wasa bane a gare ka Khaleesat, don ya basu kulawa kuma ya ba yarinyarsu attention ba abu bane da ya

kamata ki mayar issue, plsss ni ban san ki da mummunan kishi irin wannan ba gaskiya, don Allah kar ki ari halin da ba naki ba ki yafa kawata, ki zama mace ta gari me kwantar ma mijinta hankali ba wai me

ɗ

aga masa hankali ba akan abinda bai kai ya kawo ba,

da wani abu ya samu cikin jikinki kin zata bazai shiga damuwa ba, wallahi a yanxu dai kulawa da soyayya kadai Ajay ke bukata not all this things you are doing" Bude kofar parlon aka yi, Khaleesat ta jawo hijab dinta ta saka, Yaya Mustapha ya shigo parlon d

a sallama, Khaleesat ta amsa tana yi masa sannu da zuwa, da fara'a ya amsa yana kallonta yace "Hajiya Khaleesat ce a gidan namu yau?" Tana

ɗ

an murmushi tace "Ina yini Ya Mustapha?" Yace "Lafiya lau, ya kike ya kwana biyu?" Tace "Alhamdulillah" Yace "Ya mai

gidan fa?" Tace "Yana lafiya" Yace "To maa sha Allah, sannu da zuwa" Bedroom dinsa ya wuce, Safiyyah ta mike ta bi bayansa, Khaleesat ta bi ta da kallon mamaki kamar idanuwanta za su fito... Har bayan magrib Khaleesat bata ga keyar Safiyyah ba, har ta gaj

i da zaman parlorn ta tafi dakin baƙi, Safiyyah ta kasheta da mamaki sosai ba kadan ba, saboda mijinta ya dawo shi ne zata bar ta a gantale a parlor bayan tasan dalilin zuwan ta gidan, don ma bata da kudi a hannunta ne da tafiyarta zata yi kawai, wajen kar

fe bakwai da rabi yunwa ya ishi Khaleesat gashi ko kadan bata da juriyar yunwa yanxu, tashi tayi ta fita daga dakin bayan ta bude kofa a hankali, ta tafi kitchen ta debi abinci ta dau ruwa ta koma dakin, bayan ta gama cin abincin tayi sallah ta shiga banda

ki ta wanke bakinta da mouth wash da ta gani sannan ta fito ta kwanta. Washegari wajen karfe bakwai na safe Safiyyah ta shigo dakin ta tarar da Khaleesat na cin bread da ta dauko a kitchen don da yunwa ta tashi, wani kallo tayi ma Safiyyah, Safiyyah taki y

arda su hada ido tace "Ke yanxu da wuri kike bacci ashe? Jiya na shigo kawo maki abinci da fruits naga kin yi bacci, na tashe ki kika ki tashi" Khaleesat tace "Za ma ki gama kame kamen ki, wato ni zaki walakanta ki tafi ki makale wajen mijinki ki bar ni ka

mar gantalalliya a parlor ko" Dariya Safiyyah tayi tace "Ni fa waya naje ina yi da momy, duk yunwa ne yasa kike cin bread gaya, bari in maki breakfast yanxu" Bata jira cewar Khaleesat ba tayi saurin ficewa daga dakin tun kan Khaleesat tace komai, Khaleesat

ta kyabe baki, wai sai ga Safiyyah da makalewa a dakin ya Musty duk cika bakin da ta dinga yi, murmushi kawai Khaleesat tayi tana ci gaba da cin bread din hannunta. Wajen karfe sha biyu na rana Khaleesat ta shirya zata tafi gida, Safiyyah na kallonta tace

"To yanxu in kin koma sai ki ce ma su Umma ina kika kwana?" Khaleesat tace "Babu wanda zai ce min komai tunda an san da wanda na fita ai" Safiyyah tace "What if yaje can gidan yana neman ki bakya nan?" Khaleesat ta hade rai tace "Bazai ma je ba, bayan yas

an abinda ya aikata ai bazai ce zai je gidanmu ba" Safiyyah tace "Zai ma yi tunanin gida kika tafi direct" Tabe baki Khaleesat tayi ta gama yafa veil dinta sannan tace "Wai Maman Aslam fa?" Hade rai Safiyyah tayi kamar an kira enemy dinta tace "Oho" Khalee

sat tayi murmushi tace "Amma dai ba gida daya za ku zauna in kun koma Baltimore ba?" Safiyyah tace "Waye zai zauna gida daya da ita, ai ya ma dawo nan da aiki yanxu" Khaleesat ta bude ido sosai tace "Kai don Allah?" Safiyyah tace "Wallahi" Khaleesat tace "

Allah sarki...." Wayar Safiyyah ya fara ringing tana dubawa taga Ya Mustapha ke kiranta ta mike zata fita daga dakin Khaleesat ta fixgota tace "To wallahi ba ni zaki shanya ba ke me miji, dadin abun nima dai ina da mijin nan" Dariya sosai Safiyyah tayi tac

e "Mijin da kika gantalar, ni dai ki sakeni, yanxu zan dawo wallahi" Khaleesat tace "Ikon Allah, to amma inji dai ba gado daya ku ke kwana da ya Mustapha ba dai ko?" Safiyyah taki kallonta tana dariya tace "Don Allah ki sakeni, i will back soon" Khaleesat

tace "Ai kuwa sai dai Ya Musty yayi hakuri, mu je ki ma driver magana ya maida ni gida tukunna sai ki dawo ku shige daki" Khaleesat bata bar Safiyyah ta je wajen Ya Mustapha ba har sai da tayi mata rakiya zuwa compound, sannan Safiyyah tayi ma Driver magan

a yayi dropping dinta a gida.... Bayan driver yayi parking a kofar gidan su Khaleesat ta bude motar ta sauka tayi masa godiya, sauka yayi daga motar yace "Madam ta bada sako za a baki Hajiya" Zagawa yayi ya bude trunk din motar ya ciro wata babban leda ya

mika ma Khaleesat, Khaleesat ta dinga kallon ledan sannan ta amsa tana duba ciki, lokaci daya ta fahimci menene a ledan ta mayar masa tace "Don Allah ka mayar mata gida kawai" Drivern yace "Wallahi tace kar in dawo da su Hajiya kiyi hakuri" Bude driver sea

t yayi ya shiga sannan yayi ma Khaleesat sallama, ita dai kasa cewa komai tayi har ya bar kofar gidan, ta juya ta shiga gida, sai da ta shiga daki sannan ta bude kayan cikin ledan taga atamfofi ne guda biyu sai Abaya biyu masu tsada, da sauran tarkacen cik

in kayan lefe, Khaleesat tayi murmushi kawai ta ajiye kayan. Jay na zaune parlor yana operating laptop aka bude kofar parlon, daga kai yayi ya dinga kallon Ajay da mamaki, ya matsar da laptop din kusa da shi yace "Dawowa ku ka yi?" Ajay ya karasa ya zauna

kan kujera yace "Ni da wa?" Jay yace "Ina Halysaar?" Ajay ya jinginar da kansa da kujera kamar bazai ce komai ba, sai kuma yace "Ba tace sai ta haihu ba, duk bayan sati zan dinga zuwa dubata kawai" Jay dai kallonsa kawai yake, can ya mike ya karasa kusa d

a shi ya kai hannunsa jikinsa, zaunawa yayi gefensa yace "You are sick Ajay" Ajay ya

ɗ

aga kai ya kallesa, after some seconds a hankali yace "Yanda nake ji few months back haka nake ji yanxu, i couldn't breath well yesterday night" Jay yayi shiru yana kallo

nsa, can ya sauke idonsa, kana kallonsa zaka fahimci jikinsa yayi sanyi ya kuma shiga damuwa, a hankali ya tashi ya dau makullin motarsa yace "Tashi mu tafi asibiti" Ajay yace "A'a, just prescribe me medicine, I will be fine idan na sha" Yana fadin haka ya

kwanta kan 3 sitter din parlon, Jay yace "No Junaid, ka tashi mu je asibiti, this is not something we should take likely...."

HALYSAAH PAGE 215...

Khaleesat na zaune kan darduma da daddare bayan ta idar da sallan isha'i Noor ta shigo dakin rike da waya

r Umma a hannunta ta duka tana mika ma Khaleesat wayar tace "Wai Aunty tace a kawo maki waya" Khaleesat ta amshi wayar tana duba screen din ta ga Aunty Faridah ce a kan layin, ta kai wayar kunne a hankali tace "Aunty" Aunty Farida tace "Na'am, ya kike Khal

eesat" Khaleesat tace "Lafiya lau, ina yini?" Aunty Farida ta amsa sannan tace "Ya jikin naki?" Khaleesat tace "Na ji sauki Aunty" Aunty Faridah tace "Maa sha Allah, Allah ya kara lafiya" Khaleesat tace "Ameen" Aunty Farida tayi shiru at first, sai kuma ta

ce "Yauwa kina ji na?" Khaleesat ta gyada mata kai kamar tana ganinta tace "Ina ji Aunty" Aunty Faridah tace "Ai zaki iya zaman mota zuwa Bauchi gobe ko?" Khaleesat tayi shiru, haka nan kawai taji gabanta ya fadi sosai, da kyar tace "Aunty me ya faru?" Aun

ty farida tace "A'a ba wani abu bane, Junaid ne bashi da lafiya amma da sauki sosai, but since you are much better now ya kamata ki zo ki dubasa" Khaleesat bata san sanda ta mike daga kan darduman da take zaune ba bayan taji abinda Aunty Farida tace, da ky

ar ta zauna gefen gado cikin wani yanayi tace "Aunty ba shi da lafiya kuma? Me ya same shi?" Aunty Farida tace "Ke bana son hauka baki ji na ce maki da sauki ba" Khaleesat ta girgiza mata kai hawaye suka kawo idonta tace "Aunty ai yana nan kano fa" Tana fa

din haka ta mike ta nufi handbag dinta ta bude tana dubawa nawa ne a ciki, Aunty tace tace "Baki san ya dawo Bauchi ba kenan" Khaleesat ta sake kudin hannunta ko kifta idonta bata yi jin abinda Aunty Faridah tace, da kyar ta koma ta sake zama edge din gado

cike da karfin hali tace "Aunty yana Bauchi kuma? Yaushe ya je?" Aunty Farida tace "Na fa ce maki bana son hauka ko" Khaleesat ta goge hawayen da ya gangaro idonta muryarta na rawa tace "Bazan yi ba" Aunty Faridah tace "Ki ma yi tunda baki da hankali da n

utsuwa, gobe za a zo daukar ki daga Bauchi ki kasance cikin shiri" Hawaye kawai ke zuba idon Khaleesat ta kasa cewa komai, Aunty Farida tace "Kin ji abinda na ce maki?" Khaleesat tayi karfin hali tace "Na ji" Aunty Farida tace "Sai da safe, he is much bett

er now kawai ya kamata ki zo Bauchin ne ki dubasa" Sallama Aunty Farida tayi mata ta katse wayar, Khaleesat ta dora kanta saman pillow tana jin hawaye na gangaro mata a ido, wayar ne ya fara vibrate sai da ta firgita, ta dago kanta da sauri, taga Aunty Far

ida ce ke kira still,

ɗ

agawa tayi ta kai kunne amma ta kasa cewa komai har sannan hawaye bai daina zuba idonta ba, Aunty Farida tace "Kin san Allah idan kika ce zaki kamo hanya kamar wata gantalalliya a motar haya sai nayi mugun sa

ɓ

a maki, na ce maki gobe

za a zo daukar ki, idan haukan ki ya kuskura ya kai ki tasha da sunan zaki biyo motar haya za ki ga abinda zan maki" Cikin rawan murya Khaleesat tace "To Aunty" Aunty Farida ta katse wayarta, a hankali ta fashe da kuka don da Aunty Faridah bata sake kira b

a intention din dake ranta kenan dama, daren ranan bacci kaurace ma Khaleesat yayi gaba daya, yanda taga rana haka taga daren, ita da har cikin dare sai ta ci abinci yau ko yunwan bata ji tana ji ba, har sallahn asuba bata runtsa ba, karfe bakwai na safe n

a yi ta kira Aunty Farida da wayarta, har ya katse Aunty Farida bata

ɗ

aga ba, tayi mata kira ya kusa hudu babu answer, kwanciya tayi kan darduman da take zaune tana goge hawayen idonta, tayi lamo tana sauraran kiran Aunty Faridah amma shiru, a haka bacci b

arawo ya saceta a wajen.... Wajen karfe sha daya Khaleesat ta farka a firgice daga baccin da take, waige waige ta fara yi tana neman wayarta zata duba agogo taga babu wayar a kusa da ita, ta mike tsaye da sauri taga an saka mata wayar a caji, dauko wayar t

ayi, sosai gabanta ya fadi ganin miss calls din Jay biyu, bata san sanda ta duka kasa ba cause sai da taji maranta ya kulle, tafi minti biyar a duke har sai da taji ciwon da take ji ya

ɗ

an ragu sannan da kyar tayi dialing number Jay, har ya katse bai daga

ba, sai da tayi masa kira biyar bai yi picking ba, ta kira Aunty Farida ita ma har ya katse bata daga ba, sosai taji ta fara loosing mind dinta, a haka Umma ta shigo dakin ta sameta, Umma na kallonta ta nufeta tace "Lafiya me ya same ki?" Khaleesat ta kasa

daurewa ta fashe da kuka sosai tace "Umma ina ta kiran su basa

ɗ

agawa kuma" Umma tace "Su wa kike kira?" Cikin kuka tace "Su Aunty Farida" Umma tace "Ke bana son shashanci, ko daxun nan mun yi magana da Faridah" Khaleesat tace "To Umma ya jikinsa ta ce?"

Umma ta juya tace "Ban sani ba, tunda ke baki da nutsuwa a rayuwar ki, ki dinga yin abu kamar ba er musulmai ba, daga mutum bai da lafiya sai kuma ki fara abubuwa kamar warce bata san Allah ba" Khaleesat dai hawaye kawai ke zuba idonta, Umma ta fita ta bar

mata dakin. Sai da Khaleesat ta kusa samun heart attack a wannan rana don har azahar ba a zo daukanta daga Bauchi ba, ga bugun zuciyarta yaki dawowa dai dai tun daxu, duk kiran da tayi ma Aunty Farida taki daga mata waya, Jay ma har ta gaji da kiransa he

is not picking, gashi wayar Hadiyah a kulle yake, Mami kuma bata da layin da ake samunta da shi, tana ganin karfe biyu da yan mintuna taji bazata iya daurewa ba patient dinta ya kare gaba daya, ta tashi tana tafiya a hankali ta tafi parlor ta leka taga bab

u kowa a parlon, taga alamar Umma na cikin dakin Nenne, ta juya ta koma daki da sauri ta dau hijab dinta har kasa ta saka tana share hawayen idonta da bayan hannunta, ta dau handbag dinta me dauke da kudade zata fita kenan sai ga yaron Mama Shatu ya shigo

dakin ya tsaya a bakin kofa yace "Aunty ga mota babba ya zo za a tafi da ke" Khaleesat ta dinga kallon yaron. Tun da Khaleesat suka kama hanyar Bauchi ta zama restless, duk sitting position din da tayi a motar sai taji she is not comfortable, ta rasa zaman

da zata yi ta samu sukuni, a haka suka iso Bauchi wajen karfe shidda da rabi. Khaleesat wasn't even after the warm welcome da aka yi mata a cikin masarauta, inda hankalinta gaba daya yake daban, bayan ta idar da sallah ta daga kai ta kalli Mami a hankali

tace "Mami Hadiyah fa?" Mami tace "Tana can

ɓ

angaren su, bata san kin dawo ba ne da ta zo" Halysaah ta sauke kanta tace "To bari in je can din" Mami tace "Baza ki fara cin abinci ba?" Khaleesat tace "Anjiima zan ci Mami" Mikewa tayi ta nufi kofa ta fita, w

alking slowly ta tafi part din Jay, tana shiga ta tarar da Hadiyah tana sallah a parlor, ta nemi waje ta zauna da tunani iri iri a ranta ta jira har Hadiyah ta idar da sallahn, Hadiyah na kallonta tana murmushi ta mike ta koma kusa da ita ta zauna tace "We

lcome Halysaah, ya hanya? Ya kuma kika baro su Umma?" A hankali Khaleesat tace "Ya Jawwad fa?" Hadiyah tace "Ai suna asibiti basu dawo ba...." Khaleesat ta dinga kallon Hadiyah tana jin bugun zuciyarta na tsananta tace "Pls tell me, is he critically ill Ha

diyah?" Hadiyah ta sauke ajiyar zuciya tace "Da sauki ai, da muka je daxu dai bamu samu ganinsa ba i think he is sleeping" Khaleesat ta marairaice lokaci daya hawaye suka cika idonta tace "Don girman Allah ki gaya min gaskiya Hadiyah" kawai sai ta fashe da

kuka, Hadiyah ta zaro ido tace "Meye haka kuma Halysaah, na ce maki da sauki fa, ni dai ya kika baro su Umma tunda ke abun kuka baya maki wahala" dai dai nan Jay ya shigo parlon, Khaleesat ta daga kai tana kallonsa yace "Halysaah" Mikewa tayi tana kallons

a a sanyaye, yace "I am just seeing ur calls now Halysaah, ya hanya?" Ta nufesa tace "Don Allah zaka kai ni asibitin Ya Jawwad" Jay yace "To bari in yi sallah, kema ki je kiyi sallah..." Tace "Ai nayi" Yace "To zauna ki jira ni" komawa tayi ta zauna kan ku

jera ya wuce Bedroom dinsa, 30 mins ago suka dawo daga asibiti kuma tare da Ajay suka dawo yana can part dinsa yana bacci amma saboda baya son ayi interrupting masa baccin yasa

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login