Showing 300001 words to 303000 words out of 641791 words

Chapter 101 - HALYSAAH COMPLETE

03 Sep 2026

200

dole ta damu ba tunda ita tasan ukuban da ta sha gidan Awdul don bai da kunya ya kuma dawowa yace ga zance ga magana, in sha Allahu karshen

sa ne ya zo, in ma yana da mugun nufi ne a kanta to ga dai ta a Bauchi bazai kuma ta

ɓ

a sanin inda take ba" Aunty Murja ta sauke ajiyar zuciya tace "Abun kam babu dadi, Kuma Allah ya fi sa, babu abinda ya isa ya mata wanda Allah bai yi mata ba" Nenne tace "

Maza ku tashi ku tsaftace tsakar gidan can, banda ke ma ai sai dai gidan nan ya ru

ɓ

e don na lura kishiyarki akwai aukin kazanta, yarinyar can taki kuma ki kulleta a daki ki saka kwado kar ta kunyata mu idan bakinmu sun iso...." Aunty Murja dai tayi murmush

i ta tashi ta fita. Da fara'a Nenne ke welcoming din Jay da Ajay tana nuna masu shimfidar da ta masu na tabarma, shi dai Ajay kansa na kasa har ya zauna saman tabarman, Jay ma ya zauna sannan suka gaisheta, mafici take mika masu tace "Kamar za ayi ruwa dax

u kuma sai garin ya washe" Jay yace "Inda muka fito anyi ruwan" Nenne tace "Kaji ikon Allah, nan kuwa sai iska, to ya gidan da iyayen ku?" Jay yace "Alhamdulillah, ya me jiki?" Nenne tana cire bargon jikin Khaleesat tace "Ga ta nan, daga wanka daxu lamari

ya sake lalacewa" A fusace Khaleesat ta fixgo bargon daga hannunta ta kara rufe jikinta, shi dai Jay kallonta kawai yake haka ma Ajay, Nenne tace "Haka fa take idan bata da lafiya tayi ta nukurci kamar mu muka dora mata, tunda kina jin su ai daurewa zaki y

i ki tashi ki gaishe su" Jay yayi murmushi yace "Kyaleta kawai Kaka" Nenne tace "To ai shikenan..." Mikewa tayi tace "Ina zuwa" Daga haka ta fita daga dakin, Jay yace "Halysaah" Ta

ɗ

an juya ta kallesa amma bata ce komai ba, yace "Are you running temperatur

e?" Shiru tayi, ya tashi ya tafi kusa da ita ya durkusa yana kallonta, shi dai Ajay ya ciro wayarsa yana dubawa, Jay ya kai hannu forehead dinta yaji jikinta da zafi, yace "Bari a maki allura you will feel better in sha Allah" A hankali tace "Ai ban gama s

han maganin ba" Yace "Duka za a hada" Juya masa baya tayi tace "A'a ni bana son wani allura bayan ga drugs" Ajay ya wani kalleta, Jay yace "Amma alluran zai taimaka maki ai" Bata sake tanka sa ba sae ma daure fuska da tayi, ya mike ya koma ya zauna, sai ga

Nenne da kofin shayi biyu ta ajiye masu Aunty Murja na biye da ita da katon bread da soyayyen kwai lafta lafta a plate, Ajay ya kalli Jay, tana ajiyewa tace "Gashi nan yanxun nan aka soya maku, shayin ma sai tiriri yake kun ga..." Ajay yace "Ni na tashi d

a azumi yau alhamis, sai dai Jawwad" Jay ya juya ya kallesa, Nenne tace "Ai kuwa yau alhamis nima ina yi saboda ba a garina nake ba shi yasa ban yi ba" Matsar da farantin kwan tayi gaban Jay da katon bredin da kopin shayi duk ta maida gabansa, Khaleesat ba

ta san sanda dariya ya kusa taho mata ba duk da yanda take fama da kanta ganin how shock Jay was looking at Nenne, shi kansa Ajay kawai dakewa yayi, yayi keeping serious face a gefen Jay kar yayi dariya, Nenne tace "In kuma baka ci ba Allah ya sani bazan j

i dadi ba, kuma jikina zai yi sanyi" Daga haka ta nemi waje ta zauna tana jiran ya fara shan shayin, Jay ya ciro handkerchief dinsa yana goge fuskarsa, Aunty Murja ta nemi waje ta zauna ta kara gaisawa da su da fara'a sannan tace "Wani unguwa ku ke a Bauch

i?" Nenne tace "Nima dai na tambaya ranan amma bai gaya min..." Jay ya

ɗ

an kalli Ajay, shi dai Ajay babu abinda yace, Jay ya sauke idonsa ya sanar masu daga inda suka fito a garin Bauchi, Nenne ta saki baki tana kallonsu can tace "Kun hada wata dangantaka

da sarki ne?" Jay yace "Mahaifinmu ne" Wani salati Nenne ta saki saboda shock tana kallonsu tace "Sarkin ne mahaifinku?" Jay bai sake cewa komai ba, Nenne ta kira full sunan Mai martaba tace "Kuna nufin shi ya haife ku??" Aunty Murja tace "Haka fa kika ji

suka ce Nenne, ni dama ina ta kallon wannan na kusa da shi naga yana kama da yaran gidan sosai, tunda zaki ga ana nuno mana su ta waya yanxu, su dai wa ennan ban ta

ɓ

a ganinsu a waya ba" Tsabar yanda Nenne ta girgiza ta kasa cewa komai sai kallonsu Jay take

kamar ranan ta fara ganinsu, can ta ambato sunan Baban Jay me rasuwa sai kuma ta fashe da kuka tace "A sannan ina garin nan Allah yayi masa rasuwa, duk muka gigice, garin nan ya dawo shiru kamar ba kowa tsabar tashin hankali, Sarki adali me jin tausayin a

l'uma, mun yi babban rashi wallahi, kaninsa dake kan kujeran yanxu ne ban wani san sa ba, amma yanxu ace zan samu hanya wallahi zan je har fadarsa mu gaisa in saka masa albarka in masa addu'a" Jay na murmushi yace "Sai mu kai ki Kaka, ai yana nan" Nenne ta

ce "Da kuwa nayi farin ciki wallahi, sai Parida ta rakani mu je, ita wannan rubabbiyar me ciwo ta zauna a gida ba sai mun je da ita ba, ita kuma Murja tana da yarinya me shafar aljanu bata zuwa ko nan da can saboda yarinyar...." Ko rufe baki Nenne bata yi

ba sai ga yarinyar Aunty Murja na kokarin shigowa dakin, Nenne tayi wani ihuu ta dau mafici ta fara korar ta daga inda take zaune tana cewa "Fitaa, tafi kofar gida, Murja ba nace ki saka kwado a dakin ba wannan wani irin fitina ne saboda yarinyar nan nake

fargaban zuwa gidan nan wallahi" Ajay ya mike yana kallon yarinyar yace "Ta fita kuma Kaka?" Nenne tace "Ta fita mana

ɗ

an nan, er ruwa ce fa" Jay was totally speechless yana kallon Nenne, Aunty Murja ta mike zata dau yarinyar ta bar wajen Ajay yace "A'a ki

kyaleta" Sai ya karasa ya shigo da ita dakin ya zaunar da ita kusa da shi, ga shi Fes uwar ta shiryata har da su packing gashinta me uban yawa, Nenne dai sai zazzare ido take tana kallonsu don ita abun kunya ta dauka ai, Ajay ya kalli Aunty Murja yace "Ya

sunanta" Aunty Murja tayi murmushi, Nenne tayi karaf tace "Sunansu daya da Khaleesah, ita ma Hauwa ce, dama kuma sunan uwar Murjan Khaleesah ta ci, kunsan uwarta kishiya ta ce kuma mun yi zaman mutunci, Murja na da shekara biyar uwar ta mutu rikonta ya da

wo hannuna har na aurar da ita, Ali na ji da Murja kamar ni na haifeta, yanda na sha wahala Ali yayi karatu ita ma haka don sai da tayi poly kafin tayi aure, da iliminta haka da ku ke ganinta har turanci tana ji, bayan na mata aure haihuwar farko

ɗ

an ya ra

su bayan shekara hudu Allah ya bata wannan yarinya er ruwa" Calmly Jay yace "Kaka ba haka bane, ki dena kiranta da er ruwa, ita din mutum ce kamar kowa, a ƙasashen da aka ci gaba masu irin wannan lalura kulawa ta musamman ake basu, babu tsangwama babu kyar

a sai soyayya da ake nuna masu ana jan su jiki, wannan lalura tasu a likitance ita ake kira da Cerebral Palsy ba wai yan ruwa ba kamar yanda yawancin Hausawa ke kiransu wasu ma su ce ai aljani ne ya ta

ɓ

a su, to duk ba haka bane, kusan lalura ce ta ƙwaƙwalw

a wanda jariri ke samu tun yana cikin mahaifiyarsa ko kuma bayan an haifesa, kyara da tsangwamar masu irin wannan lalura da ake yi yana jefa iyayensu cikin damuwa, duk da yanxu kai ya waye hakan ya ragu ba kamar da ba, don haka Kaka don Allah wannan yariny

a soyayya take bukata da kulawa ba tsangwama ba, haka Allah ya so ya ganta, mutanen dake kewaye da ita sai su ja ta jiki su nuna mata so da kulawa" Nenne ta sauke ajiyar zuciya tace "Ai shikenan, mu ce mana ake yan ruwa ne zamanin mu, amma tun da ba haka b

ane ko ta shigo na dena korarta sai dai Allah ya kiyaye mu kar ta mana barna mu shiga uku" Ajay yayi murmushi kawai ya kalli Aunty Murja da kanta ke kasa yace "In sha Allah za a duba mata Wheelchair that will improve her mobility, da abubuwa da suka kamata

" Mami ce zaune tare da Mai martaba a parlonsa, bayan sun gaisa tace "Dama Allah ya taimake ka akan maganar Jawwad nace bari in sameka, bayan sun dawo ya kawo min maganar wata yarinya da yake so da aure, duk da nasan kun yi magana da shi kafin yayi da ni,

to nayi masa fatan alkhairi, shi ne yanxu na same ka inji what is ur take on the matter" Mai martaba yace "Ai mun gama wannan maganar, har nayi ma wakilai na maganan tafiya wajen iyayen yarinyar, akan haka ake yanxu" Mami tayi shiru tana kallonsu, can ta g

yara zama tace "Amma Ranka shi dade ban tari hanzarin ka ba, daga magana sai tura wakilai na zata ai sai anyi bincike me zurfi kafin tura wakilai" Mai martaba kallonta kawai yake don dama ta saba fada masa duk maganar da ya zo bakinta, can ya sauke ajiyar

zuciya bayan kusan minti daya yace "Kina ganin zan tura zuwa gun iyayen yarinyar babu bincike Fulani?" Mami tace "To naga abun yayi gaggawa ne ranka ya dade...." Mai martaba yace "To haka muka shirya Fulani" Tace "To yanxu har an tsaida ranan zuwa Kanon ke

nan?" Mai martaba yace "Kwarai kuwa... Nayi wasu baƙi zan je in same su yanxu Fulani" Yana kai wa nan ya mike ta bi sa da kallo har ya fita daga parlon.

*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah*

Ur evidence via 07087865788

HALYSAAH

PAGE

9

3

Jay na zaune parlon Maminsa ta dalilin kiransa da tayi, ko minti talatin basu yi da dawowa gidan tare da Ajay ba don yau ma sun je duba Khaleesat, Mami ta kallesa tace "Ina kuma yake jan ka kuke tafiya duk kwana biyun nan daga safe zuwa dare" Jay ya d

aga kai ya kalleta, sai kuma yace "Yake ja na kuma sai kace wani yaro Mami?" Mami tace "To ai hakan kake a wajensa, ba kai ne Drivern sa duk inda za shi a garin nan ba" Jay bai sake ce mata komai ba don tunda suka fara zuwa unguwan da Halysaah suka sauka A

jay ne ke driving din, Mami tace "Daxu Me martaba ke gaya min yanda ku ka yi da shi, dama da ban je na samesa ba kawai sai dai inji magana a sama, kai menene dalilinka na ƙin gaya min yanda ku ka yi da shi? Kun je kun yanke shawara har za a zartar amma ni

ba a fita hakkina an sanar min ba and you are okay with that" Jay dai yayi shiru don he was only following Ajay's advice, Mami tace "To ai shikenan, Allah Ubangiji yayi mana me kyau" Jay yace "Ameen" Mami tace "To a tudun yolan wace unguwa suke?" Jay ya da

ga kai ya kalleta yayi shiru, tace "Ko ba Tudun yola ka ce ba?" Yace "Eh can suke, amma ban rike address din gidan ba ai, any problem Mami?" Mami tace "A'a wai in ji, amma tunda baka sani ba ai shikenan" Wayarsa ne ya fara ringing yana dubawa yaga Mai mart

aba ke kiransa, ya daga kai ya kalleta yace "Mai martaba na kirana" Mami tace "Ohk" Mikewa yayi ya fita daga parlon, after a while ta tashi zata fita sai ga Aunty ta shigo, dama kuma wajen nata zata je don gaba daya akanta tayi relying all this while tunda

tace ta bar mata komai, Mami ta koma ta zauna tace "Kuma gun ki zan tafi yanxu" Zaunawa Aunty tayi tana murmushi tace "Toh albishirin ki, yanxu haka na samo Address din gidansu yarinyar a wajen Mai martaba, ashe daga Kano zai wakilta aje gidan nasu, iyaka

mutane biyu ne za su tafi daga nan" Mami tace "Da gaske kin samo Address din?" Aunty tace "Kwarai kuwa, ce masa nayi mijin er uwata dake Tudun yola yace min a basa address din gidansu yarinyar in dai Tudun Yola suke kilan bazai rasa sanin Ubanta ba tunda

duk sun san kansu a unguwan, tun da safe muka yi hakan da shi shine ya kira Jawwad din ta waya a gabana ya tambayesa Address din, nan take kuwa ya gaya masa, sannan Mai martaba ya sake nanata min address din, ina komawa parlona na rubuce address din a waya

don kar in mance, to na fita ne, sai yanxu na dawo shi yasa ban shigo na sanar maki ba" Mami tayi shiru tana kallon Aunty, can tace "Amma kinsan yanxun nan Yaron nan ya fita a parlon nan ina tambayarsa Address din yace bai sani ba???" Aunty ta ta

ɓ

e baki t

ace "Ai ko ya gaya ma Mai martaba daxu da safe" Mami tayi wani murmushi tace "Ki bar ni da shi, in yasan wata ai bai san wata ba" Aunty tace "Ba nace ki fito masa a mutum ba kin ki kina gudun bacin ransa, tun yaushe za ki ce masa bai isa ba kuma hakan ya z

auna" Jay na zaune gaban Mai martaba a parlonsa, Mai martaba was quiet for a minute kafin yace "Jawwad..." Jay ya daga kai ya kallesa don sai da gabansa ya fadi cause Mai martaba da serious tone ya kirasa, a nutse Mai martaba yace "Me yasa baka gaya min ya

rinyar da kake nema ta ta

ɓ

a aure ba?" Jay ya dinga kallonsa babu ko kiftawa zuciyarsa na bugawa, Calmly Mai martaba yace "Ko ba haka bane?" Sauke kansa ƙasa yayi ya kasa cewa komai at first, shi gaba daya mance Khaleesat ta ta

ɓ

a wani aure yake yi, lokaci d

aya yaji jikinsa yayi sanyi sosai, ya dafe kansa da yayi masa nauyi a take, Cikin kwantar da murya Mai martaba yace "Ba hakan zai sa in hanaka aurenta don ta ta

ɓ

a aure Jawwad, my concern is why did you hide this important thing away from me? Idan da ban sa

an min bincike kafin in tura zuwa ga mahaifin yarinyar ba da sai in wakilai na sun je mahaifinta zai sanar masu matsayin yarinyar kenan? Or probably kun ma riga kun hada plan ace budurwa ce duk ban sani ba... kuma duk hakan zai iya yiwuwa tunda har ka iya

boye min, Kai ba aure ka ta

ɓ

a ba Jawwad, this is ur first marriage idan Allah ya tabbatar, ka kuma san yanda al'adar gidan nan yake, tun asali da ka sanar min cewar ta ta

ɓ

a aure ai sai an fara auren ka da Hadiyah idan ya so ko bayan wasu watanni ne sai ka

auri ita wannan din, nobody will question you Jawwad, an sanar min abubuwa da yawa a binciken nan da na sa aka min wanda ina ga babu amfanin in zauna ina zayyano su a nan, har ma unguwan da suka baro kafin su dawo tudun yola na sani, just that I was taken

aback knowing so many things.... kawai dai nasan ni bazan hanaka aurenta ba tunda kace kana sonta Ahmad, although bayan binciken nan da aka min akwai abubuwa da yawa wanda na kasa fahimta har yanxu, ban san ko da wani abu da ku ke boye min kai da Junaid b

a, ko kuma akwai wani abu da ku ka juya kai da shi akan lamarin nan, anyway... ba hakan zai sa a fasa zuwa gun mahaifinta gobe asabar kamar yanda na tsara ba, sai dai za a fara zuwa gun dangin uban Hadiyah tukunna, so dalilin kiran ka kenan Ahmad, Allah ya

maka albarka...." Jay dai ya kasa

ɗ

ago kansa don gaba daya jikinsa yayi sanyi qlau, kenan an sanar ma Mai martaba karatun da take a Amurka ma Saurayi ne ke sponsoring dinta tun bai aureta ba, bayan nan ya gano shi da Junaid suka ci gaba da dawainiya da it

a a Amurka kenan bayan mutuwar aurenta? Yanxu har labarin prison din da aka kai babanta da dalili duk yaji, ta yaya ma har aka gano tsohon unguwan da suka baro?? Babu abinda ya kara sanyaya masa jiki sai batun gidan da ya siya masu don ya ma san har shi za

a gaya ma Mai martaba kawai bazai dai ce masa komai bane, tun da gashi yace yaji abubuwa da yawa, Mai martaba ya katse masa tunaninsa yace "Ko da wata maganar da zaka yi ne Ahmad?" Da kyar ya

ɗ

ago kai, cikin sanyin murya yace "Kayi hakuri Abba, nayi kusku

re boye maka duk abubuwan nan da nayi tun farko, a gafarce ni Abba" Mai martaba ya

ɗ

an yi murmushi yace "It's fine Ahmad, i only called to correct you, in sha Allah bikin ma baza a saka lokaci me tsayi ba, kawai asalin mahaifin yarinyar ne ake contemplatin

g har yanxu, ance Kano kuma aka dawo aka ce Bauchi... How true is that? Although ba mu ji daga mahaifin nata ba har yanxu ai, mahaifiyarta kuma aka ce buzuwa ce er Nijar ko?" Da kyar Jay yace "Haka ne, Mahaifinta a Kano aka haifesa amma asalin babansa

ɗ

an

Bauchi ne, zama ya maida shi Kano, daxu kakarta ke sanar mana don tana garin nan,

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login