Showing 198001 words to 201000 words out of 641791 words
bangon gidan ki sai yayi kanshi, muna zuwa ko wani gari
don yin gyaran jiki
n Amarya.
08093772168
Karku manta munada mayukan gashi masu Kara tsawon gashi zasu gyara miki gashi yayi laushi yayi tsantsi,Sannan yayi tsawo in two months.
Muna tura kayan mu duk inda mutum yake, location dinmu Maiduguri ne. 08093772168
HALYSAAH 62
S
au daya Khaleesat ta kallesa ta dauke kai bayan tayi convincing kanta ba wajensu yake tahowa ba, Safiyyah tayi kasa da murya tace "Ni ban ma ta
ɓ
a ganinsa a school din nan ba sai yau, gwara Housemate dinki shi dama ya saba zuwa ya same mu a nan sanda muke E
xam, he is coming toward us fa" Ita dai Khaleesat bata ce komai ba amma can kasan ranta ita ma tayi mugun mamakin ganinsa a department dinsu, how did he even know spot din da suke zama da Safiyyah, sai kawai tayi assuming hanya ce ta biyo da shi ta nan din
, har ya iso inda suke zaune Khaleesat bata daga kai ba but she is surprise, Safiyyah na kallonsa tana murmushi tace "Good afternoon Ya Junaid" Ba tare da ya kalleta ba yana kallon different direction yace "Evening, can you excuse us... I want to have a wo
rd with ur Coursemate" Safiyyah dai bata fasa kallonsa ba tana gyada kai tace "Sure, why not...." Sai kuma ta dau jakanta ta mike tana kallon Khaleesat tace "Zan je wajensu Nora, if you are looking for me ina can..." Khaleesat ta gyada mata kai kawai, daga
haka Safiyyah ta bar wajen, ita dai Khaleesat mamaki ma yasa ta kasa kallon Ajay dake tsaye kanta, he wants to have a word with her? To me zai ce mata da zai biyota har department din su, duk da under same faculty suke amma ko da wasa bata ta
ɓ
a haduwa da
shi a school ba in ba few days ago ba da suka shigo da Jay, ta kalli wayar da yake mika mata fuskarsa babu yabo babu fallasa, she was surprise, why is he giving her his phone? bata amshi wayar ba ta daga kai ta kallesa a karo na farko, ganin yanda ya daure
fuska ya sa ta mika hannu ta amshi wayar tana kallon screen din, sosai gabanta ya fadi ganin hoton da suka yi da Aymaan jiya a get together, ta dinga kallon hoton babu ko kiftawa, gashi ba hoto daya ba ba kuma biyu ba, can ta kalli a ina yaga hoton sai ta
ga a Instagram ne, bata san sanda ta gyara zama ba zuciyarta na bugawa sosai, Instagram kuma? Me ya kai hoton Instagram? ta shiga uku, ita da ko a screen din wayarta bata ta
ɓ
a saka hotonta ba balle aje ga WhatsApp ko kuma facebook uwa uba Instagram, gaba d
aya hankalinta yayi mugun tashi ta kasa cewa komai, da kyar ta daga kai ta kallesa ta ga wani irin kallo yake mata, ta sauke idonta gabanta na ci gaba da faduwa ta kasa cewa komai, fixge wayarsa yayi daga hannunta yace "So you came back fully prepared to p
arty in Baltimore Right? You came back to mingle with jobless guys following them to party up and down, Har kin ma mance abinda ya same ki, but wait... Baki ta
ɓ
a zuwa islamiyya bane ko kuma kin je kin yi skipping classes? Ko kuma bayan mijin da kika ce a k
yaleki kina son zama da shi ya sake ki baki zauna kin tambayi makusantan ki what next ba? Kawai saboda kina jin kanki on a different level yanxu shi yasa kika kama hanya kika tafi cikin kattin banza masu shaye shaye da sunan get together, har ki tsaya gefe
n wannan crook guy din ayi maku hoto kina dariya" Khaleesat ta kasa daurewa ta fashe da kukan da tun safe take son yi bata samu kwakkwaran reason din yin sa ba, shiru yayi yana kallonta irin kallon mamakin nan, after a minute ya zauna inda Safiyyah ta tash
i amma bai ce mata komai ba, ita kuma bata fasa kukan da take ba kamar an aiko ta, tayi me isarta don kanta ta hakura ta fara goge idonta tana sauke ajiyar zuciya, sai a sannan ya kalleta yace "Ohk i understand, kin dawo America ne kiyi abinda ranki yake s
o ba kuma kya bukatar wani yace zai yi questioning din ki ko kuma yayi correcting din ki" Wani sabon kukan ta fara yi kamar ana tunzurata, ya mike trying to control himself yace "Get up" ganin taki tashi ya hade rai yace "Baza ki tashi ba?" A hankali ta mi
ke tana ci gaba da goge hawayen dake zuba idonta tana shesshekan kuka, babu yabo babu fallasa yace "Mu je" Bata masa musu ba ta fara bin sa har sannan tana goge hawayen idonta, after almost 10 minutes walk suka iso inda yayi parking motarsa, yana bude mota
r ta daga kai ta kallesa a hankali tace "Ni ban ce ma Safiyyah zan tafi ba" Ya mata wani irin kallo yace "Baza ki ce mata ba, get in the car" Bata ce komai ba ta zaga ta bude gaban motar ta shiga, bata ta
ɓ
a shiga motarsa a America ba sai ranan, har suka is
a Apartment dinta babu abinda yace mata, bayan yayi parking without looking at her yace "Leave my car" Sauke idonta tayi, ta bude motar a hankali ta sauka ta kulle masa tana kallonsa tace "Don Allah tunda ka san sa kayi masa magana ya goge hotona a Instagr
am" Ya jefa mata wani kallo yace "Zan gaura maki mari, ni na hada ku nayi maku hoton da zan ce masa ya goge?" Daga haka yayi Reverse yayi zoom off daga Neighborhood din, wasu sabbin hawaye suka cika idonta ta juya tana tafiya a hankali ta nufi kofar apartm
ent dinta ta bude ta shiga, zaunawa tayi a parlor ta fara tunanin to ko shi ma Housemate dinta ya ga hoton ne a Instagram bayan status din Safiyyah, bata ta
ɓ
a jin haushin Safiyyah irin yau ba, Allah kadai yasan mutane nawa ne suka ga hoton nan daga jiya zu
wa yau, ta goge idonta ta bude handbag dinta ta ciro wayarta ta fara kiran Safiyyah, yana fara ring Safiyyah ta daga tace "Ya tafi ne in fito?" Trying to be calm Khaleesat tace "Kin ga Safiyyah kije kiyi ma wannan mutumin magana ya cire hotona a Instagram,
who does that? Ta yaya daga hoto zai je yayi posting a Instagram kamar mun san juna from anywhere da shi? Meye hadina da shi da zai min haka? Har wani dogon magana muka yi da shi da har zai dau hotona tare da shi yayi posting a Instagram dinsa?" Muryarta
na rawa ta kare maganar, Safiyyah tace "Innalillahi, Instagram yayi posting hotunan? Kinsan ni ba wani damuwa da IG nayi ba, kuma fa Aymaan ban ta
ɓ
a ganin yayi posting mace a Instagram ba, sai gashi yayi posting na ki, amma how did you know his Handle da h
ar kika ga yayi posting din ku?" A fusace Khaleesat tace "Ina ruwana da wani handle dinsa, kawai daga haduwa ko maganar minti daya ban yi da mutum ba ya kama hotona yayi posting duk duniya su gani, is he even okay? Ko ba shi da hankali ne? To wallahi ki je
kiyi masa magana ya goge min hotona" Safiyyah tace "Ni ma dai nayi mamaki gaskiya, wallahi ban ta
ɓ
a ganin yayi posting mace ba sai gashi yayi posting din ki, kar dai shi yasa Ajay ya zo wajen ki yau? Don definitely za su iya sanin juna kilan ma suna follo
wing juna, kinsan akwai association na Nigeria student a makarantar mu dole ma za su sun san juna,
ɗ
an Deputy governor ne fa Aymaan, he is also popular on IG" Takaici ya sa Khaleesat ta katse kiran ta jefar da wayarta kan kujera, wani mugun haushin Aymaan
da Safiyyah ta dinga ji a ranta, da tana da numbersa babu abinda zai hanata kiransa ta gaggaya masa magana, ko an gaya masa ita irin wa ennan matan ne da har zai yi posting din ta duniya su gani, Abdul ne ya fado mata, nan da nan jikinta yayi mugun sanyi,
don babu uban da ya kai sa zama active a Instagram gashi da uban followers, wa ma ya sani ko yasan Aymaan din, sosai taji hankalinta ya tashi ta jinginar da kanta da kujera wasu hawayen na zuba idonta, bata ta
ɓ
a jin Safiyyah bata kyauta mata irin yau ba, d
a kyar ta mike ta dau jakarta da waya ta wuce sama. Meemah ce ta shigo dakin Momy tana mika mata wayar hannunta hankali tashe tace "Momy kin gane wacece wannan kuwa?" Momy ta ajiye bowl din farfesun hannunta ta amshi wayar tana kallon screen din, can ta ka
lli Meemah tace "Wannan ba er matsiyatan can bace? Khaleesat take ko wa" Meemah ta zauna gefen gado har sannan fuskarta dauke da tashin hankali tace "Ita ce Momy, ita da Aymaan" Momy ta ajiye wayar ta dau bowl din farfesunta ta ci gaba da ci tace "Waye kum
a Aymaan?" Meemah tace "Aymaan din kuma kika manta yau Momy, Muhammad Aymaan
ɗ
an mataimakin gwamna fa" Momy ta kalleta tace "Wai tsohon saurayin ki Muhammad?" Meemah ta hade rai tace "Tsohon saurayi fa kika ce Momy, Aymaan din ne tsohon saurayina?" Momy ta
ce "To in ban ce maki tsohon saurayin ki ba ya zan ce, yaron da ba
ɗ
aga kiranki yake ba yanxu, yaushe rabon ki da shi? kin ga kuwa ai sai in ce tsohon saurayin ki Meemah, dama ai a titin Instagram din ku ka hadu da shi, ba sai da na dinga hada maki da roko
n Allah ba kika samu sassaucin son sa da kika dora ma kanki, dama su biyu zuciyarki ta makale ma da shi da wani
ɗ
an sarki yake ko wa shi ma kullum sai kin isheni da zancensa bana ma tunanin kina da numbersa, duk samarin ki a Instagram din ku ke haduwa kuma
a can ku ke rabuwa, ni na ta
ɓ
a ganin wannan wahala" cike da damuwa Meemah tace "Wallahi mace ce ta shiga tsakaninmu da Aymaan Momy, amma ai ya so ni kamar ran sa, ki tuna har fa kano ya sha zuwa wajena" Momy ta tabe baki tace "Amma ai ba gidan ubanki yake
zuwa ba sai dai yace ku hadu gidan cin abinci ko wani wajen, bai ta
ɓ
a biyo ki yaga gidan ku ba, shekara kusan takwas ana abu daya in da gaske son naki yake me ya hanasa fitowa har yau, ni dama tun da Malam Tasi'u yace min bazai fa aureki ba na hakura da k
ashe kudina a iska, amma ai na kashe kudi kan wannan Aymaan din, bayan Malam Tasi'u ma akwai wani malamin da yace min mu hakura ba auren ki zai yi ba bata maki lokaci kawai yake, kuma uwarsa ma a tsaye take kyam" Meemah tace "Momy duk ba wannan ba, a ina y
asan yarinyar nan har suka yi hoto tare? Kinsan shi ma a Amurka yake kuma makarantar su daya amma ya gama degree dinsa tuntuni in dai ba masters ya koma yi ba, kuma wnn hoton daga gani a Amurka aka yi sa" Momy tace "Atoh kika san ko tsohon hoto ne, dama ai
kin ce iskanci ta dinga yi a Amurkan don haka ba abun mamaki bane don kin ga hotonsu tare, yanxu kuwa ai sai dai tayi karuwancinta da yan Mariri" Meemah dai ta kasa cewa komai amma kana ganinta kasan hankalinta ya tashi sosai, Momy ta kalleta tace "Ai kun
ma fi shekara biyu baku yi waya da shi ba ko?" Meemah ta sauke wani ajiyar zuciya tace "Yanxun ma ina ganin hoton na kirasa bai daga ba, amma ni abinda ya bani mamaki duk yanda yake da mace fa baya posting dinta ko a WhatsApp balle har Instagram" Momy tac
e "Ɗan wani gari ne ma?" Meemah tace "Gusau" Momy tace "Abdul ya san sa ne?" Meemah tace "Oho, shi wannan ana sanin cikinsa ne, ni ban san ko sun san juna ba, kuma ai Abdul bai san ni da Aymaan ba tunda kinga ba wai ya ta
ɓ
a zuwa gidanmu bane Aymaan din, sa
i dai su san juna a Instagram amma ba a sarari ba" Meemah ta kara Zooming din hoton da kyau tana kallon tsadadden Abayan jikin Khaleesat ga wani kallo da Aymaan ya kafeta da shi, ita kuwa tana dariya with her beautiful set of teeth, Meemah ta fice daga waj
en hoton ta sake dialing number Aymaan amma har ya katse bai daga ba, mikewa tayi ta nufi kofa, Momy ta tabe baki tace "To ke banda abunki me zai yi da er talakawa aka ce maki, in kin bibiya hoton ya dade, yanxu kuwa ina taga hanyar zuwa Amurka, ai uwarsa
ma ta fi mu ƙin talakawa bari ki ji in gaya maki, a zamanin yanxu dai ko wani me kudi ya waye baya yarda ya hada zuri'a da talaka, yanxu kwarya tabi kwarya kawai, haka abun yake" Ita dai Meemah ta fice daga dakin tana sake dialing number Aymaan with confus
ion. Tana zaune usual spot din da suke zama a school tana jiran Safiyyah da taje kai ma wani coursemate dinsu laptop dinsa, tun daxu take zaune wajen tana danna wayar hannunta with full concentration, lkci daya ta dakata da abinda take yi a wayarta jin wan
i kamshin turaren da ta sani ya doki hancinta, waige waigen wajen ta fara yi suna hada ido bata san sanda ta saki wayar hannunta ba zuciyarta na bugawa tana kallonsa babu ko kiftawa, he was the least person she is expecting to see in her life, lkci daya ta
ji wani courage ya zo mata ta dau wayarta fuskarta a daure ta mike da nufin barin wajen, ya fixgo gyalen jikinta yana kallonta da kyau yana murmushi yace "You think i will let you just like that Khaleesat? Har kin samu masu ci gaba da sponsoring din ki an
dawo dake America, ga shi har ana hoto dake ana dora ki a Instagram, u snapped a picture together with Aymaan har yayi posting din ki duniya ta gani, ko wani
ɗ
an iskan gaye kin sani a Amurka and they are all ready to go through any mile for you, to ki sani
na maida aurenmu da ke, you are still my wife...." A firgice Khaleesat ta farka daga baccin da take ta mike zaune jikinta na rawa, tun da uwarta ta haifeta bata ta
ɓ
a mummunan mafarki irin wannan ba, ta sauka daga saman gadonta har sannan jikinta na rawa,
bata san sanda ta fashe da matsanancin kuka ba tana ganin abun kamar ba mafarki bane gaske ne, ba karamin tashin hankali ta shiga ba ta fara karanto duk addu'an da ya zo bakinta tana kuka, duk yanda ta so ta samu nutsuwa hakan ya gagare ta, she was really
shock, da kyar ta daure ta dauko wayarta ta kunna data hannunta na rawa, kawai taji she wants to speak with her Housemate, tana bude data taga Aunty Farida ta ajiye mata sako, ta shiga DM dinta taga hoton da suka yi da Aymaan ta turo mata tana tambayar wan
ene shi, kuma me yasa zata yi hoto da shi.... Tashin hankalin Khaleesat ya ninku akan wanda take ciki da, she was so confuse and shock, gashi jikinta sai rawa yake, a ina kuma Aunty Farida taga hoton nan, ta shiga uku, shikenan kilan Abdul ma zai gani kena
n mafarkinta ya tabbata ya zamto gaskiya? Ta fashe da matsanancin kuka tana jin zuciyarta kamar zai fito tsabar tashin hankali, ko reply din Aunty Farida bata yi ba ta fita daga WhatsApp din ta fara dialing number Housemate dinta da sauri, ta kirasa har sa
u biyu bai daga ba, rasa yanda zata yi tayi tana kuka, can kawai ta fara dialing number Safiyyah har sannan jikinta bai dena rawa ba, yana fara ring Safiyyah tayi picking, cikin rawan murya Khaleesat tace "Safiyyah baki ce ma mutumin nan ya goge hotona a I
nstagram ba dama??" Safiyyah tace "A'a na masa message ta WhatsApp he is not online fa, na kuma kirasa bai yi picking ba, kuka kike yi ko me? Haba Khaleesat sai kace warce tayi wani mugun abu? Get together fa kawai muka je aka yi hoto ba wai club ba, kuma
shigar ki ta mutunci kika yi fa, Aymaan kuma left a reasonable distance tsakanin ku balle ace ko manne maki yayi a jiki" Khaleesat taki bata amsa tace "Kina da number Ya Junaid pls?" Safiyyah tace "Eh kamar ta numbersa Jawwad yayi min fowarding receipt din
10M da aka tura ma su Maman Abdul" Da sauri Khaleesat tace "Don Allah ki turo min yanxun nan" Safiyyah tace "Ohk bari in duba, amma ni dai wallahi ban ga abun damuwa ba don kawai Aymaan ya daura hoton ki a Instagram, sanannen Celebrity ne shi fa, kawai do
n bama Instagram ne shi yasa baza mu sani ba, kuma kawai don dai kina Iddah ne da ace kin gama so what?? Ai kin isa ne yasa ya dora ki" Khaleesat ta katse wayarta don bata son ta gaya ma Safiyyah magana she is just controlling her self all this while, ba a
dau lokaci ba sai ga Safiyyah tayi mata fowarding number Ajay, Khaleesat tayi dialing number da sauri, gaba daya zafi ta dinga ji duk da uban sanyin da ake har da snow, don Ajay na dropping dinta daxu babu dadewa aka fara snow shi ne har ta kwanta bacci t
ayi wnn mummunan mafarkin, sai da ta kira sau biyu sannan Ajay ya daga,