Showing 408001 words to 411000 words out of 641791 words
na tsaye parlor tace "Ya jikin nasa?" Khaleesat ta duka nan kasan carpet ta gaisheta sannan tace "Da sauki" Mami tace "Har yanxu baccin yake?" Girgiza kai Khale
esat tayi tace "A'a ya tashi" Mami tace "Ok" Ta karasa cikin Bedroom din, ita dai Khaleesat bata mike daga inda take durkushe ba, Mami ta karasa har kusa da gadon dakin tana kallon Ajay da ya mike zaune ganinta, tace "Ya jikin?" Ya gaisheta sannan yace "Da
sauki" Mami tace "Allah ya sauwake" yace "Ameen" After some minutes ta Juya ta fita daga dakin ta koma parlor tana kallon Khaleesat tace "Yaushe Jawwad ya sa masa drip din?" Khaleesat ta girgiza kai tace "A'a ba shi yasa masa ba, wani Dr ne" Mami tayi shi
ru bata ce komai ba, can ta nufi kofa, Khaleesat ta bi ta da kallo har ta fita daga parlon sannan ta mike a hankali ta koma cikin Bedroom din, jingina tayi jikin gadon tana ta zaune har bacci ya dauketa a haka, Ajay ya juya yana kallonta, sai kuma ya mike
zaune yayi disconnecting din drip din hannunsa ya dau pillow ya ajiye kusa da ita, da hannu daya yayi using yayi laying dinta down the bed, ta bude ido da sauri, sai kuma tayi lamo kan pillown tana kallonsa, ya maida drip din hannunsa, lumshe ido tayi bacc
i ya kara dauketa. Sai kusan karfe tara Khaleesat ta farka taji yana wanka a bandaki, ya cire drip din da ko rabi bai kusa ba, ta cire duvet din da ya rufa mata ta sauka daga kan gadon ta fara gyaran babban dakin, Ajay na fitowa bathroom ko goge jikinsa ba
i yi ba taga ya kwanta kan gadon da ta gama gyarawa covering himself with duvet, ta ajiye turaren wutan hannunta da ta saka a burner ta koma kusa da shi tana kallonsa tace "Me yasa zaka yi wanka yanxu..." Juyawa tayi jin sallama a parlor sai kuma ta kalli
Ajay that was shivering, ta tashi da sauri ta tafi ta bude press din kayansa, ta dauko masa one among the many jallabiyas she saw in one part of the press, ta dawo kusa da shi ta cire duvet din jikinsa ta mika masa jallabiyansa sannan ta fita daga dakin ji
n wani sallaman, Walid ta gani tsaye parlor taji gabanta ya fadi sosai, ta
ɗ
an koma baya ta sauke kanta kasa cike da karfin hali tace "Ina kwana" Shi dai kallonta kawai yake daga sama har kasa da idanuwansa kamar wanda ya sha wani abu, sai kuma taji yace "
Tare mu ke da Mai martaba, he is here to check on ur so called Husband...." Ta gyada kai without saying anything, Walid ya
ɗ
an yi murmushi still looking at her ya juya ya fita daga parlon, ita kuma ta koma daki tana kallon Ajay da ya daure ya saka jallabiy
ansa tace "Mai martaba ne zai shigo" Daga haka ta koma parlor ta tsaya gefe tana jiran shigowan Sarki, after almost 3 minutes suka shigo parlon, da Mai martaba da Walid sai Jay da Mukhtar, ta duka har kasa tana gaida Mai martaba ya amsa yana tambayarta me
jiki, kanta a kasa tace "Da sauki ranka shi dade" ita dai tana durkushe inda take har suka karasa cikin Bedroom din. Throughout ranan haka Khaleesat ke zaune gefen gado kusa da Ajay Wanda baccinsa yafi rashin baccin nasa yawa, abinci kusan kala uku ta diba
r masa a wanda aka kawo masu part din amma bai ci ko daya ba sai fruits kawai da ya sha, da rana Mami ta sake shigowa dubasa bata yi minti uku ba ta fita, sai Mukhtar da shi ma ya shigo bayan la'asar, amma bata ga Jay ya dawo bangaren ba tun bayan da suka
zo tare da Mai martaba wajen karfe tara, Yakumbo ma na ta shigowa bangaren ta tambayi Khaleesat ya jikinsa, Khaleesat sai tace mata da sauki, wajen karfe shidda ta sake shigowa Khaleesat ta fito parlor tana kallonta don wannan shi ne shigowarta na kusan go
ma kenan ranan, Yakumbo ta zauna kasa ta sinne kai da ladabi tace "Allah ya taimake ki, har yanxu Yariman bacci yake?" Khaleesat tace "Ehh bacci yake" Yakumbo na
ɗ
an kame kame tace "Dama idan ba damuwa ina son wata er magana dake ne, Allah ya sa bazai
ɓ
ata
maki rai ba kuma Allah sa ki fahimce ni ranki shi dade" Khaleesat tace "To ina ji, ki zauna kan kujera mana Mama" Yakumbo ta girgiza kai da sauri tace "A'a nan ma ya isa ranki shi dade, ni dai fatana Allah sa ki fahimce ni don a dar dar nake son maki wann
an maganar, kuma ki dubi Allah maganar nan ya zama tsakaninmu ki gafarceni ranki shi dade ban san ko maganata ta karshe tayi tsauri ba, Allah ya taimake ki" Khaleesat ta zauna gefen kujera tana kallonta tace "To ina ji Mama" Yakumbo tayi kasa da murya tace
"To Nagode Gimbiya, ni dai kamar yanda na gaya maki kwanaki kwarai a gidan nan na taso tun ina karamata, a lokacin mahaifiyata na da rai tana matsayin jakadiyar marigayiya mahaifiyar Yarima, don haka hatta ni mahaifiyarsa ta nuna min soyayya sosai, a maga
na ta gaskiya ranki shi dade duk abinda ke faruwa gidan nan kusan babu wanda ban sani ba, na dade ina son sanar maki cewar ciwon nan da Yarima yake da zarar ya shigo gidan nan a gaskiya har da sa hannu ba ciwon tsakani da Allah bane, jifa ne, tun wancan lo
kacin da aka kawo ki nake son inyi maki maganar nan amma ina tsoron yanda zaki dau maganata, to a takaice abinda nake son ce maki yanxu shi ne a duk sanda ya dawo masarautar nan idan baya da lafiya kai koma da lafiyarsa ni ke kawo masa abinci ko kuma na ka
wo masa kayan shayi da ruwan zafi kuma akasari ni ke hada masa abun shan sa saboda yarda da yayi da ni, ki gafarceni ranki shi dade ni dai a duk sanda bai da lafiya nakan zuba masa wannan a shayinsa...." Yakumbo na magana ta fito da kullin maganin tana nun
a ma Khaleesat, amma fa duk a tsorace take tana kallon Khaleesat dake ta kallon kullin maganin, sai kuma tayi kasa da murya ga tsoro kwance fuskarta karara tace "Wallahi ranki shi dade ba komai bane illa itatuwa na kaikayi koma kan mashekiya, kuma hadi ne
na musamman wallahi, duk naje garinmu nake amso masa wajen kanina don lakani ne da kakanmu ya bar mana, to in sha Allahu Yarima na shan shayin nan kafin kwana biyu zaki ga ya mike kamar ba shi ba, wani lokacin a ranan ma zaki ga alamar samun sauki tattare
da shi, bai ta
ɓ
a sanin wannan abu da nake yi ba kinsan
ɗ
an boko ne ina fargaban yanda zai dau lamarin duk sanda ya sani shi yasa nake kaffa kaffa ban ta
ɓ
a gaya ma kowa wannan sirrin ba, to yanxu tunda kece matarsa kinga ke ce ke hada masa shayi ko wani abu
da zai sha don ba hurumina bane hakan yanxu, idan ma baki yarda ba yanxun nan sai in zuba a ruwa in sha, wallahi bana nufinsa da komai sai alkhairi, da mugun abu ne kin san bazan zo in gaya maki ba kuma duk hanyar da zan bi in zuba masa a abinci to zan bi
in zuba babu kuma wanda zai sani" Khaleesat dai sai kallon kullin maganin take yi babu ko kiftawa, har cikin ranta kawai taji ta yarda da Yakumbo, can ta amsa maganin tace "To shikenan zan hada masa shayin da shi in sha Allah Mama" Sosai farin cikin fuska
r Yakumbo ya kasa boyuwa tace "To Allah ya kara girma ranki shi dade tun jiya nake son maki magana amma ina tsoron yanda zaki dau maganar, na fi shekara uku ina ma Yarima haka, duk ranan da na tabbatar zan zuba masa maganin sai in dafa shayin da kayan kams
hi sosai ta yanda bazai ji kamshin maganin ba, Yarima zagaye yake cikin makiya da mahassada bai da wani masoyi da ya wuce Mai martaba sai Jawwad a gidan nan, rayuwarsa na cikin mugun hatsari a gidan nan, ba sai na bude baki na gaya maki wasu abubuwan ba da
kanki duk zaki fahimta daya bayan daya" Khaleesat dai ta sauke idonta bata ce komai ba, sallama aka yi kofar Parlon, Khaleesat ta maida maganin bayanta da sauri ta boye ganin har za a bude kofar parlon, Yakumbo kuwa sai zare ido take a
ɗ
an tsorace, Hajiya
A'isha da Kilishi ne suka shigo parlon sai Hajiya Habiba, suka dinga bin parlon da kallo a walakance, Yakumbo kuwa ta
ɗ
aga hannu daya sai jero masu kirarin ban girma take daga inda take zaune kanta a kasa, Khaleesat ta gaishesu babu wanda ya amsa mata cik
insu suna tafiya cike da kasaita da gadara suka nufi dakin Yarima suka shiga suka kullo kofar, Yakumbo ta kalli Khaleesat da sauri tayi kasa da murya tace "Ranki shi dade ki dinga kulle kofar da makulli sai ki ce masu shi ya kulle kayansa daga ciki in dai
ba idonsa biyu ba, shigar wasun su cikin dakin nan ba alkhairi bane wallahi, babu abinda baza su iya yi ba, yanxu da kiyi dubara ki bi su ciki" Khaleesat dai tayi shiru, sai kuma ta gyada kai tace "To Mama" Yakumbo ta mike still murya can kasa tace "Kiyi k
okarin hada masa shayin yau da maganin don Allah, shi yasa ma na taho da matacin da zaki ta ce shayin da shi in kin zuba" Daga haka tayi ma Khaleesat sallama cikin girmamawa ta fice daga parlon, Khaleesat sai kallon kofar dakin take ganin har yanxu basu fi
to ba, kasa daurewa tayi ta mike ta nufi cikin dakin ta bude ta shiga, duk ta samesu tsaye sun zagaye gadon suna kallonsa, shi ko yaki bude ido duk da shigowarsu dakin sai da ya tashesa daga baccin da yake amma he still pretends he is sleeping, duk suka ju
ya suna kallon Khaleesat da ta shigo, da wani expression Kilishi tace "Ko baki da hankali ne yarinyar nan, muna ciki zaki shigo saboda rashin kunya? Ba a koya maki ladabi bane a gidan ku? Ko mu din sa'an iyayenki ne?" Khaleesat ta sunkuyar da kanta, Ajay y
a bude idonsa ya mike zaune fuskarsa daure to stop them from saying more to her, Kilishi bata sake cewa komai ba ganin ya tashi zaune, Khaleesat dai ta juya a hankali ta fita daga dakin, Hajiya Habiba na kallon Ajay tace "Sannu ya jikin?" A takaice yace "N
a ji sauki, Alhamdulillah" Hajiya A'isha tace "Allah ya sauwake" Daga haka ta juya ta fice daga dakin, Hajiya Habibah ta bi bayanta, Kilishi ma tayi haka, duk suka koma parlorn, Hajiya A'isha na kallon Khaleesat strictly tace "Idan kika ce a haka zaki zaun
a cikinmu wallahi sai zaman gidan nan ya gagare ki, this house will be nothing but a living hell for you tunda naga alamar ke din mara tarbiyya ce mara kunya er kananun mutane baki san na gaba da ke ba, ke har er gidan uban wacece:ma tukun kike neman goga
kafada da mu, ko 'ya yanmu har ki mutu baki isa goga kafada da su ba balle mu, amma mu zuba da ke a gidan nan" Hajiya Habibah tace "Gaskiya sai an gyara mata zama yarinyar nan naga tana da rawan kai, kin san
ɗ
an talaka sannan gata bazawara, don sabuwar ama
rya bazata ta
ɓ
a wannan rashin
ɗ
a'an ba" Daga haka duk suka fita daga parlon, Khaleesat dai bata dago kanta ba, can ta mike a hankali zata hada masa shayin da Yakumboo tace ta hada masa.
HALYSAAH
Khaleesat na shiga dakin rike da cup din shayin da ta hada
ta tarar da Ajay zaune drip na biyu dake hannunsa ya kusa karewa, ta zauna gefen gadon tana kallonsa tace "I made this tea for you" jin yayi shiru tasan next reply dinsa cewa zai yi bazai sha ba, hakan yasa ta hau saman gadon ta zauna dab da shi ta debi s
hayin a spoon ta hade rai ta kai masa baki tana kallonsa tace "Sai ka sha fa tunda na hado" Dariya ma ta basa amma bai yi ba ya kauda kai yace "Ni nace maki zan sha shayi?" Ta hade rai sosai tace "Wallahi sai ka sha ni bazan zubar ba" Ya
ɗ
an kalleta yace "
To ke ki sha mana" Tura masa spoon din tayi a baki har shayin spoon din ya zuba kan farin rigar jikinsa, ya jawo tissue dake bedside drawer da sauri yana goge gaban rigar yace "Ke" Ko sauraronsa bata yi ba ta sake diban wani zata kai masa baki, dariya ta b
asa sosai, ganin kar taje ta kwara masu shayin dake tiriri a cup yasa ya amshi cup din ya fara shan shayin, ita dai tana zaune kusa da shi tana kallonsa, har ya sha rabi ya ajiye sauran ta girgiza kai tace "Ai shanyewa zaka yi wallahi" knocking da taji yas
a ta sauka daga kan gadon ta fita, Jay ta gani da Hadiyah a parlon, tun dawowarsu sai yanxu taga Hadiyah, suna hada ido Hadiyah ta wani hade rai ta kauda kai tana taunar chewing gum, Jay yace "Is he sleeping?" Khaleesat ta girgiza kai tace "A'a" dakin ya n
ufa Hadiyah ta wani harari Khaleesat ta bi bayansa tana makale da shi, tunda Ajay ya hada ido da Jay ya dau sauran shayin da ya ajiye yana sipping, Jay dai ya tsaya few steps away from the bed bai dai ce komai ba, sai Hadiyah ce tace "Sannu yaya, ya jiki?"
Ajay na shan shayin hannunsa without raising his head yace "Alhamdulillah" Tace "To Allah ya sauwake, ya sa kaffara ne" Yace "Ameen" Bayan minti uku Jay ya juya ya nufi kofa ya fita daga dakin, Hadiyah tayi ma Ajay sallama sannan ta bi bayansa, Ajay ya aj
iye cup din hannunsa don har ya shanye shayin bai ma sani ba. Bayan isha'i Ajay ya shiga wanka, Khaleesat ta fara tidying dakin zata kunna turaren wuta duk da it's very clean, taji ana sallama a parlor again, fita tayi zuwa parlon gabanta ya fadi sosai gan
in Walid a tsaye, yana kallonta ya nufi Bedroom din Ajay yana leka ciki a hankali, ganin babu kowa a dakin sai ma da yaji kamar Ajay yana cikin bandaki sai ya dawo cikin parlon ya nufeta yana kallonta yace "Ina mijin naki?" Komawa baya ta fara yi taki cewa
komai gabanta na faduwa ganin irin kallon da yake mata, kawai taga ya mika hannu zai rikota, tsabar tsoro and her mind was already in a state of readiness da abinda zai iya faruwa kawai ta wani turasa da karfi, sai gashi rigijib kan kujera, shi kansa he w
as very shock cause he didn't see that coming, bai ta
ɓ
a tunanin zata turasa ba har yayi loosing balance ya fadi, tuni Khaleesat ta fice daga parlon da sauri, Walid ya bi ta da kallo baki bude ko motsawa bai yi ba a inda ya fadi, tana waige waige ta nufi pa
rt din Mami da saurin ta, Mami na zaune parlor tare da mai taya ta aiki dake mata kwadon zogale a gabanta don tafi son a hada mata shi tana kallo, ga zogalen yaji uban tsire da kayan hadi, kana gani kaga rich zogale, parlon duk ya gauraye da kamshi, da ido
Mami ta bi Khaleesat da ta sunkuyar da kanta ta karaso cikin parlon ta zauna kasa tana gaida Mamin, Mami ta amsa tace "Jikin nasa ne har yanxu?" Khaleesat ta girgiza kai tace "A'a da sauki, kawai zuwa nayi" Mami bata sake ce mata komai ba ta maida attenti
on dinta kan abinda ake hada mata har mai aikin ta gama sannan Mami ta dau plate ta dibi zogalen ta dora fork a gefen plate din tace ma mai aikin "Mika mata" Mai aikin ta amsa ta mika ma Khaleesat plate din zogalen da ladabi, Khaleesat ta amsa tayi godiya,
Mami ta debi wani madaidaici a karamin warmer ta ajiye sannan ta dibar ma mai aikin nata, Hadiyah ce ta shigo parlon, tun da ta shigo take kallon Khaleesat daga sama har kasa, sai kuma ta nufi dakin Mami without saying anything to anyone, Mami ta bi ta da
kallo kamar bazata ce komai ba sai kuma dai tace "Me zaki dauka?" Ko juyowa Hadiyah bata yi ba tace "Sako aka aiko ni in dauka" Daga haka tayi shigewarta dakin Mami, Mami tayi shiru har sannan bata dauke idonta daga kan kofar dakin ba, can sai ga Hadiyah
ta fito rike da wayar Jay dake dakin, Mami tace "Saboda zaki dau masa waya shi ne zaki wuce min daki babu magana babu komai Hadiyah, duk yau mun hadu dake ne halan?" Hadiyah taki juyowa tace "To ai shine dai ya aikeni ba wai kawai na shiga dakin bane haka"
Tana fadin haka ta fita daga parlon, Mami dai bata ce komai ba, ta maida zogalenta da zata ci gefe, ta sallami Mai aikinta, Mai aikin ta mike ta fita daga parlon, Khaleesat ta fara cin zogalenta tana kallon Film din da ake yi a TV dake parlon, after almos
t 10 mins Mami ta dau wayarta ta fara dialing number Jay, amma da ya shiga sai a danna mata busy, ta kira ya kusa sau biyar ana danna mata busy daga karshe ta ajiye wayar kawai a gefenta, bayan Khaleesat ta gama cin zogalen ta kalli Mami dake zaune ita dai
ba kallo take ba amma idonta na kan TV, Khaleesat ta mike ta dau wani plate da aka yi