Showing 177001 words to 180000 words out of 641791 words

Chapter 60 - HALYSAAH COMPLETE

03 Sep 2026

232

fara auren sa wallahi" Don mamaki Umma ta ma rasa abun ce masu ganin yanda suka juya zancen lokaci daya, yau ga fadan karfin hali tana gani kiri kiri, biyesu ma bata lokaci ne kawai a

wajenta ga makota na jin su, tsam ta mike tayi shigewarta daki, Khaleesat ta mike ta bi bayanta. Washegari da sassafe Umma da Aunty Farida suka fito tsakar gida suka tarar da Mama Zubaida da Mama Shatu a tsaye suna jiran fitowarsu za a je ba Nenne hakuri,

ko wanne da Hijab dinsa har kasa don sanyi ake sosai, duk abinda suka yi ma Umma jiya hakan bai sa tace bazata bi su zuwa gidan Nenne ba, Su ma din sun san ta dalilin Umman sai Nenne ta iya hakura ta sa Malam Ali ya maida Mama Shatu shi yasa Mama Zubaida d

a kanta ta samu Umma ko kunya babu tayi mata magana wajen karfe biyar din asuba, Mama Shatu dama a makota ta kwana ranan don sae da Nenne ta dawo ta korata har da watsi da en tsummokaran ta, sae kusan hudun asuba Shatu ta dawo gidan daga inda ta kwana, a h

aka duk suka kama hanya zuwa gidan Nenne da asuban. Ranan Thursday da safe Khaleesat na zaune dakin Umma tana kallon Aunty Farida dake ta jera mata kayanta da aka amso wajen guga a cikin akwati, ita dai Khaleesat har sannan ta rasa gane me take ji a ranta,

farin ciki take ko akasin haka duk ta kasa ganewa, babban damuwarta yanxu bata san da idon da zata kalli Housemate dinta ba idan ta koma America, sannan gani take kamar babban burden kawai zata zame masa a can din tunda ita ba komai gare iyayenta da za su

tallafa mata da shi ba idan ta koma,

ɗ

an kudin dake account dinta ba wani kudin kirki bane kuma da shi ta siya sabon waya with new sim card, sai few abubuwan da tasan zata bukata a can kasar, sauran kudin dake account dinta ko dubu dari da hamsin bai kara

sa ba, duk wannan tunanin yasa take damuwa sosai a ranta, Aunty Farida ta daga kai tana kallonta kafin ta rufe zip din jakar tace "Baki manta komai ba dai ko?" Khaleesat ta gyada mata kai kawai, Aunty Farida tace "A Airport din za ku hadu da Safiyyah goben

?" A hankali Khaleesat tace "Eh" Aunty Farida ta kulle zip din tace "Gwara ki saki ranki kiyi abinda ke gaban ki Khaleesat, ki cire duk wani damuwar dake ranki kar ki je ki samu matsala a karatun ki, shi kuma Jawwad Allah ya saka masa da mafificin alkhairi

...." Khaleesat ta sauke idonta bata ce komai ba, lkci daya taji hawaye ya cika idonta, Aunty Farida ta mike ta dauko daya akwatin don hada few foodstuffs din da suka siyo mata da Umma wanda zata iya shiga Amurka da shi, a hankali Khaleesat tace "Toh Aunty

ta yaya za a maida masa kudinsa dake account dina?" Aunty Farida ta daga kai ta kalleta, can tace "Kudin wa? Ko Abdul?" Khaleesat ta gyada mata kai, Aunty Farida ta saki baki, can tace "Wai dama har yanxu kudaden nan nasa na account din ki?" Khaleesat ta

gyada mata kai, shiru Aunty Farida tayi kamar me nazari, after a while tace "Ki ci gaba da ajiye kudin kawai Khaleesat, duk sanda ya dawo ya bukaci kayansa sai a basa, ko Umma kar kiyi ma maganar kudin for now, bana son a samu delay a tafiyarki don yanxu s

ai su iya cewa sai an maida masa kudadensa, kuma hakan zai iya ja maki delay...." Ita dai Khaleesat bata ce komai ba, Aunty Farida ta ci gaba da hada foodstuff din da take a akwati.

*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur e

vidence of payment 07087865788

👈🏻

, it's better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*

_Assalamu Alaikum yan mata da matan Oga ina me maku albish

ir da cewa Han-Ash skin beauty ta zo maku da kayan gyaran jiki iri iri wanda zai mayar da fatarki kamar Madara ta yanda duk inda kika shiga sai an kalleki, ki sai mayukan da zesa fatar ki tayi kyau, muna kuma maraba da siyan daya ko sari, i am assuring you

that duk wani product dinmu is tested and trusted, ga kuma arha, for more information contact Han Ash via 0902 469 2720_

We sell all kind of children school shoes, school bag, Lunch box, Readymade for children.... Atamfa, Lagos laces, veils, Handbags,

shoes, lafaya, jewelries, kitchen items e.t.c.....

All at affordable prices

Akwai adashin kayan kitchen, kayan yara and atamfa with laces if interested....

Follow this link to join my WhatsApp community: https://chat.whatsapp.com/B5uR4Jfj6fZIIN0EIIHeg

M

HALYSAAH 55

Wajen karfe uku na yamma Khaleesat na zaune bakin kofar dakin Umma Aunty Farida na combing din mata dogon gashinta bayan ta wanke mata shi da Shampoo da Conditioner, har wani sheki baƙin gashin nata yake yi bayan Aunty Farida ta shafa mata

man gashi, tun daga wajen wanke gashin Aunty Farida ke ta mata fadan ta bar gashinta ya kakkarye saboda banzan da tayi da shi ta dena kula da shi, ita dai Khaleesat bata ce mata komai ba don har sannan basu san irin zaman da tayi a gidan Abdul ba, don ma a

bun ya tsaya iya kakkaryewan gashi, har bata son tuna experience dinta a gidan Abdul hakan yana traumatizing dinta, su Mama Zubaida da Mama Shatu dai na bakin murhu suna girka abincin siyarwansu na yamma, suna yi suna kuskus a bakin murhun, lkci lkci sai s

u kalli direction din su Khaleesat, ita dai Aunty Farida dama ko kallo basa isanta a gidan, a da dai ta biye su har dambe sun sha yi amma yanxu bata da wannan time din, kallon stark illiterates kawai take masu, wasu mata biyu ne suka shigo gidan babu ko sa

llama, sun yi shiga ta alfarma sun sha gwala-gwalai suna taku cikin isa, at the same time suna bin ko ina na gidan da kallo cike da kyama gashi dama su Mama Zubaida sun yi gaje gaje da ruwa a tsakar gidan ranan, Khaleesat ta dinga kallonsu haka Aunty Farid

a da ta ajiye comb din hannunta, Mama Zubaida ta mike tace "Sannun ku da zuwa ko dai batan hanya ku ka yi ne, in gidan Hajiya Samira matar Alhaji Bala ku ke nema can karshen layi za ku karasa sai ku yi tambaya a nuna maku gidan, amma ba nan bane" Momy ce t

a shigo gidan tana tafiya gansan gansan da Drebanta a bayanta yana biye da ita, mayafin nata ma ko yafa shi bata yi ba, gashi ta sha wani tsadadden baƙin glass no respect, Khaleesat ta dinga kallonta babu ko kiftawa, lkci daya taji gabanta ya fadi sosai, t

a juya ta kalli Aunty Farida, sai ga Meemah ita ma ta shigo gidan tana yatsine fuska, ita ko mayafin ma babu a hannunta, Aunty Farida ta dake tace "Bayin Allah lafiya? Daga ina haka, babu ko sallama" Daya daga matan da suka shigo da farko tana ma Aunty Far

ida wani matsiyacin kallo tace "Ba shi ya kawo mu ba, a irin wannan bolan za ayi maku sallama?" Umma ta fito daga dakinta don tana jin duk abinda ake cewa, tsaye tayi bakin kofa tana kallonsu, Mama Shatu da Mama Zubaida dai sai zazzare ido suke kamar wa en

da suka yi ma sarki karya, Momy ta karaso har tsakiyar compound din tana tafiya cikin isa da gadara, fuskar nan nata babu ko digon mutunci tace "Zuwa nayi in ji ko shegiyar er ku tana da gadon Abdul ne, Ko kuma shi ma satan da ku ka yi ma ubansa kuke da ni

yyar za ku yi masa, in kuwa babu gado to yanxun nan ba sai anjima ba a maido mana kudadensa dake account din er ku..." Umma ta kalli Khaleesat nan da nan hankalin Umma ya tashi sosai, Aunty Farida tace "Ikon Allah, shi ne sai anyi wannan zuga haka kamar za

ayi yaki?" Meemah ta matso har gaban Aunty Farida tana mata matsiyacin kallo tace "Yakin ne ai, ko kin ga alamar da sassauci muka zo? sanin halin familyn na ku na sata wanda ku ka gado a gun Malam me dattin hula ya sa mu ka yo tattaki a mayar mana da kuda

den mu tun wuri, ai kowa yasan sata da cin amana shi ne tambarin gidan nan, don haka tun wuri ba a jiyo kan mu ba a maido mana Miliyan goman Abdul, kun zata bulus za ku ci ga banza ta fadi ko? To Sponsoring din matsiyaciyar er ku da ya dinga yi da kudinsa

ma ai ba yafewa yayi ba sai kun biyasa a lahira wallahi, kawai babban farin cikin dake saka ni nishadi idan na tuno shi ne karewar da zata yi as dropout din John Hopkins university, don ko kaf zuri'arku za ku siyar baza ku samu kudin biya mata ta ci gaba d

a karatun a kasar Amurka ba, da yau ta gama John Hopkins sai bakin ciki ya kasheni, amma Alhamdulillah a dropout zata kare, Abdul kuma ya yar da kwallon mangwaro ya huta" A fusace Momy tace "Ke Meemah tsayuwa cikin kangon bolan nan ne ke burge ki da baza k

iyi abinda ya kawo mu mu fita ba, ko so kike Cholera ya kama mu? Ina ke ina cacar baki a irin wannan gida" Aunty Farida tayi wani murmushi tana kallon Meemah tace "Sai dai kuwa bakin cikin nan ya kashe ki don kina ji kina gani Khaleesat zata gama karatu a

makarantar da kike fada, Allah ya ji ƙan ki in Advance" Cikin tsawa Meemah tace "Keee, ki iya bakin ki, kar ki gan ni tsaye a wannan bolan gidan a gabanki kiyi zata ni sa'ar yin ki ce, don wallahi inda na bi da kafata ma baki isa ki bi ba har duniya ta nad

e, ni ba sa'ar ki bace ta ko wani angle, banda Abdul yayi downgrading dinmu ya kaskantar da darajan da Allah yayi mana ina mu ina hada hanya da matsiyata talakawa irin ku balle har aje ga auratayya? Ke ki duba irin wajen da ku ke rayuwa wanda ko karen gida

nmu baza mu bari yayi rayuwa a cikin wannan hali ba, To wallahi ki iya bakin ki ni ba sa'ar yin ki bace, ba karamin aikina bane in sa a shafe babin ki a duniya" Tun kan Aunty Farida ta mayar ma da Meemah amsa Umma ta hanata, cikin fushi Aunty Farida tace "

Kamar yaya in yi shiru Umma, gidanmu fa suka zo suka same mu kuma ki ce inyi shiru? ashe ma karyar arziki suke in don saboda miliyan goma za su yi wannan uban zugan kamar masu bibiyan miliyan 50 har su tsaya suna kumfar baki suna tada jijiyoyin wuya akan 1

0M, uban wani ya saka ya tura mata kudin a account dinta da har za su zo nan suna gaya ma mutane maganar banza, ko kuma rokonsa tayi ya saka mata kudin, su arzikin ma wallahi da gani taka haye suka yi, da can su ma matsiyata ne" Meemah ta mika ma Momy hand

bag dinta tana huci zata cakumo Aunty Farida, Momy ta dakatar da ita tace "Ke me ya kai ki, ki ta

ɓ

a ta ki ce kin ta

ɓ

a wa? Salon ta goga maki ƙashin tsiyarsu kike kokarin dambe da ita? Yanzu wannan har Class din damben ki ce in ba rashin wayo irin naki ba M

eemah? Ai ba a dambe da talaka matsiyaci" Umma ta kalli Khaleesat tace "Ta yaya za ki fiddo kudaden a account din ki Khaleesat?" Khaleesat ta sauke idonta tace "Sai naje banki, bani da Atm card, kuma kudin bazai fita lokaci daya ba...." Momy na mata matsiy

acin kallo tace "Sai ki tashi ki tafi bankin ai don wallahi kudaden nan baza su kwana a account din ki ba yau, da niyyar ki kin ci bulus tunda ubanki ne ya nema masa kudin ba" Khaleesat ta daga kai ta kalleta, ita har sannan ta kasa daina mamakin matar nan

, kai tunda aka haifeta ma ita ba a ta

ɓ

a shayar da ita ruwan mamaki yanda mahaifiyar Abdul ta shayar da ita ba, yau sati daya da sakin da Abdul yayi mata amma kullum in ta tashi sai ta zauna tayi mamakin uwarsa ganin abun take kamar Drama, ba ayi ranan da

zai zo ya wuce da Momy bazata fado mata ba, bata ta

ɓ

a san akwai mutane irin Momy a rayuwar nan ba, muryar Mama Zubaida taji tace "Ai ba zama zaki yi kina zazzare ido ba kamar barauniya, tashi za ki yi ki kama hanya ki tafi banki ki fiddo masu da kudadensu

tunda ba gadon Abdul din gare ki ba kuma ba kudin tsohon ki bane, duk wani abu na rashin gaskiya dake da uwarki da kanwarta gaba ku ka basa ba baya ba, banda haka ta yaya za kuyi shiru da makuden kudadensa har Miliyan goma a account dinki? So ku ka yi ku d

anne kudin ko yaya? Don ma kun samu masu hakuri da kawaici da wasu ne idan ba a zo da motar yan sanda an tafi da ku ba ku ce bani ba, wannan ai rashin gaskiya ne da rashin tsoron Allah kiri kiri, duk kun yi mukus da bakin ku za ku cinye miliyan goma ga ban

za ta samu" Aunty Farida ta juya tana kallon Mama Zubaida, sai kuma ta nufeta tana cewa "Zubaida idan ban zubar maki da hakora a gidan nan yau ba ki ce bani ba, don kaza kazan ki akwai tsinannen da ya sako bakin ki? Uwarki muka yi ma rashin gaskiya ko uban

ki?" Mama Zubaida tayi wani shewa tana tafe hannu tace "To yau kika saba Farida? Ai ke fitsararriya ce dama mara mutunci mara kunya shi yasa ga ki har yau duk kyan ki kin rasa mashinshini sai dai kiyi tuwo tuwo a garin legas kina hadawa da karuwanci, waye

bai san wannan ba?" Aunty Farida zata cakumo Mama Zubaida Mama Shatu ta shige tsakaninsu tace "Ke yanxu Farida Zubaida sa'arki ce zaki dinga zaginta haka ta uwa ta uba don kawai tana kishiyar yayarki? Daga dai ta fadi gaskiya banda

ɗ

an Adam baya son gaskiy

a?" Aunty Farida tayi wani wurgi da Mama Shatu sai ga ta a kasa timmm, tuni Mama Zubaida ta shige dakinta ta kulle kofarta da sakata tana cewa "Haka kawai ki shafa min bakin jini irin na ku? Allah ya sauwake in yi dambe dake Farida, ku je can ku ji da rash

in sa'ar ku a rayuwa, ku kenan daga wannan iftila'in sai wannan bala'in, ko wani fitinar duniya a kan ku ya kare, daga wannan sai wannan, Allah kadai yasan laifin da ku ka tafka a kasar ku, kilan ma ta zina aka sami ke da yayar taki, ga bakin jini da rashi

n sa'ar ku ya shafi Malam ya talauce" Da kafa Aunty Farida ta hambare uban miyan da Mama Zubaida ke yi na abincin siyarwanta, miyar duk suka malale kasa, shinkafar ma dake cikin kwando ta kifar da shi a kasa tana zagin Mama Zubaida ta uwa ta uba, Mama Shat

u ganin yanda aka yi watsi da kayan sana'an Mama Zubaida ya sa ta ja bakinta tayi shiru ta tafi gun nata miyan ta zauna tana cewa "Hakuri kawai za kiyi Farida, hakan ba dadi kam" Momy ta rike ha

ɓ

a tace "Alhamdulillahi da na yi iya bakin kokarina na ganin b

an hada iri da gayyar tsiya ba, ku kuga wannan tsiya haka kamar 'yar tasha, ga talauci ga tashanci, Abdul ya so ja mana abun fade a dangi Allah ya takaita min abun, kuma ba dai kun ce kudade na banki ba, to zuwa yau da daddare in ga alert din Miliyan goma,

in kuwa ba haka ba gobe da sassafe za ku gan ni a gidan nan ba kuma zuwan lumana zan yi ba, ai shi ramin karya kurarre ne, kuma ko kwabo daya yayi ciwon kai a kudaden nan wallahi sai an daure er ku..." Momy na kai wa nan ta bude handbag dinta ta ciro taka

rda dauke da account details dinta ta jefa ma Khaleesat sannan ja tawagarta suka yi waje tana cewa "Haka kawai Meemah zata ja min bala'i ta hada ƙashi da wannan iri na fitina, irin tsiya, to kiyi dambe da ita ki ce kin yi dambe da wa? Kina ganin yarinya ka

mar mahaukaciya, A'a wallahi Allah ya maki tsari" A haka duk suka fita daga compound din, Khaleesat taji hawaye ya cika idonta, Umma komawa dakinta tayi tayi tagumi ranta ba dadi, ita kam ta gode Allah da jarabawa iri iri, daga wannan sai wannan, Khaleesat

ta dau takardan da Momy ta jefa mata ta juya ta shiga dakin Umma hawaye na zuba idonta, Aunty Farida kuwa bata fasa zage su Mama Zubaida da Mama Shatu a tsakar gida ba, Mama Zubaida taki fitowa kuma taki tanka Aunty Farida, Mama Shatu kuwa tayi tsit kamar

bata san da wa Aunty Farida take ba, daga karshe bayan Aunty Farida tayi masu wankin babban bargo ta shige dakin Umma tana huci, Umma ta daga kai tana kallonta tace "Yanxu ban isa ince ki bari ki bari ba Farida?" Aunty Farida ko tanka Umma bata yi ba ta d

au Hijab dinta ta saka tana kallon Khaleesat tace "Ki tashi ki shirya mu tafi bankin" Mikewa Khaleesat tayi tana goge idonta ta dau hijab dinta ta saka, a haka suka kama hanyar banki da Aunty Farida, amma suna isa bankin suka tarar an tashi aiki sai ran Mo

nday don

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login