Showing 348001 words to 351000 words out of 641791 words

Chapter 117 - HALYSAAH COMPLETE

03 Sep 2026

240

ba, yana isa gabanta ya mika mata ledan, bata yarda ta hada ido da shi ba ta amshi ledan a hankali tace "Nagode" Kamar jira yake yace "Kazamar mace ce kawai bata san when her period

is going to be due ba..." Yana fadin haka ya juya ya bar wajen, ta bi sa da wani harara tana turo baki, daga karshe dai suka yi boarding jirgin da zai kai su Maryland wajen karfe takwas saura na safe, after 8 hours trip kuma suka sauka airport din Baltimo

re, sosai Khaleesat tayi farin cikin ganin Safiyyah da ta zo tarbanta a airport har da tsadadden bouquet of flowers dinta, Khaleesat ta rungumeta tare da flowers din looking so happy, Safiyyah ta bi Ajay da ya wuce su da kallo baki bude, can ta kalli Khale

esat tayi kasa da murya tace "Shi kuma wannan fa? Har da shi ku ka dawo dama?" Sai kuma ta fara kalle kallen inda zata hango Housemate shi kuma, ganin bata ga alamar sa ba tace "Ina Housemate din?" Khaleesat ta kasa ce mata komai tana kallonta, lokaci daya

hawaye suka cika idonta, da mamaki sosai Safiyyah tace "Kuka kuma? Me ya faru? What's happening?" Khaleesat ta rungumeta hawaye masu zafi na zuba idonta ta fara shesshekan kuka, Safiyyah was speechless at first ta ma rasa ta ina zata fara magana don duk z

urfin tunaninta bata kawo dalilin kukan Khaleesat a ranta ba a wannan lokacin, ta dago kanta tana kallonta tace "Tell me what is happening mana pls Khaleesat? Ina Housemate din? Ko dai ba ayi auren bane tukunna? but ke kika ce min an daura ai, and that was

the last time we chatted, da naga baki online since after then nayi chatting Aunty Farida tace min ai har an kai ki Bauchi" Khaleesat ta fara goge hawayen da ya ki tsaya mata, ganin ba magana zata yi ba kawai Safiyyah ta kama hannunta suka bar wajen, suna

tafiya a hankali cikin sanyin murya Khaleesat tace "Sophie, Housemate isn't my husband!" Safiyyah ta tsaya ta juya tana kallon Khaleesat da sauri babu ko kiftawa tace "I don't understand" Khaleesat ta sauke idonta wasu hawayen na sauka idonta da kyar tace

"Yes, he isn't" Safiyyah that was so confuse tace "Then who is the Husband? Don Allah ki gaya min Khaleesat...." Khaleesat ta kasa cewa komai hawaye sai kai kawo suke a idonta taki dago kanta, A hankali Safiyyah dake gwalo ido tace "Ajay?" Khaleesat ta da

ga idanuwanta ta kalleta with more tears rolling down her cheek ta gyada mata kai trying not to burst into cry, kallonta kawai Safiyyah take babu ko kiftawa kana ganinta kasan ba karamin girgiza tayi ba a inda take tsaye kamar warce ruwa ya cinye, they sto

od there for more than 3 minutes babu wanda yace komai cikinsu, Safiyyah was just staring at her kamar gunki don ko kwakkwaran motsi bata yi, ita kuwa Khaleesat sai share hawayen da yaki tsaya mata kawai take, daga karshe Safiyyah ta kama hannunta a hankal

i suka ci gaba da tafiya slowly, kana ganin Safiyyah kasan she is more than shock and speechless at the same time, tsaye suka samu Ajay jikin motar da zai kai su gida ya rungume hannu fuskarsa babu yabo babu fallasa alamar su yake ta jira, driver din da ya

zo daukansu daga gida har ya gama saka traveling luggages dinsu gaba daya a bayan mota, Safiyyah na kallonsa with calmness tace "Ina yini, ya hanya?" Ajay yace "Alhamdulillah" Ta juya ta kalli Khaleesat da idanuwanta har sun yi jajir saboda kuka tana

ɗ

an

murmushin karfin hali tace "Kawata zan koma can gida in dauko abincin da na girka, i will call you to know where to bring the food for you" Kai kawai Khaleesat ta gyada mata, Safiyyah ta kalli Ajay tace "To sai anjima, zan je in dauko mata abinci a gidanmu

" Ba tare da Ajay ya kalleta ba yace "Ohk, you can get in the car and tell the driver ur Address" Daga haka ya zaga ya shiga front seat, Safiyyah ta

ɗ

an yi jim, can kuma dai ta bude bayan motar, sai da Khaleesat ta fara shiga sannan ita ma ta shiga ta kull

e motar, a haka suka bar airport din, dai dai gidansu Safiyyah Drivern yayi parking bayan ta nuna masa sannan ta kalli Khaleesat tace "Ina zuwa" Bude motar tayi ta sauka ta nufi apartment dinsu, few minutes later sai ga ta ta fito da warmers din abinci biy

u Khaleesat ta bude mata door din motar ta amshi warmers din ta ajiye su tana kallon Safiyyah a hankali tace "To ki shigo" Safiyyah ta

ɗ

an kirki murmushi bayan ta saci kallon Ajay ta gefen ido tace "A'a ki dai je gida ki huta, ko gobe sai in zo in sha Alla

h" Nan da nan hawaye ya cika idon Khaleesat tana kallonta pleadingly alamar ta shigo motar, Shi dai Ajay ko kallonsu bai yi ba, Safiyyah ta sauke boyayyen ajiyar zuciya ganin hawayen idon Khaleesat ta kara satan kallon Ajay, sai kuma ta zaga ta daya side d

in motar ta bude ta shiga ta kulle sannan driver ya ja motar suka bar unguwan, wajen karfe biyar suka isa gidansu Ajay, bayan driver yayi parking a parking lot Ajay ya bude motar ya nufi entrance din gidan, Safiyyah ta bi sa da kallo sai kuma ta ta

ɓ

e baki

tana gyada kai murya can kasa tace "Tab

ɗ

ijam" Bude motar tayi ta sauka rike da warmer daya na abinci, Khaleesat ma ta sauka tana rike da handbag dinta da dayan warmer din, a haka suka nufi cikin gidan driver na biye da su da traveling boxes dinsu, suna shi

ga babban parlorn suka tarar da babu kowa ciki, but everywhere was sparkling clean ga wani daddadan kamshi da parlon ke yi, Safiyyah ta zauna kan kujera tana kallon Khaleesat tayi kasa da murya tace "Khaleesat how did you agree to this? Menene ya faru har

haka ta kasance? Dama ana switching aure all of a sudden just like that? Bar masa ke Jay din yace yayi kenan? Kuma me ya janyo hakan? Cewa yayi yana son ki shi ma shine Jay ya hakura? Da wani bakin ya iya budewa ya fadi hakan? Bai ji kunya ba? Budurwar bro

ther dinsa fa? Does this look normal at all? Ke da wani ido kike kallon Jay yanxu? Shkkn wannan ne makomar azababben soyayyar da ku ka yi da Jay kenan? Is this how everything ended? Ko dai kuskure aka yi gun daurin auren aka daura da shi cikin rashin sani

sai kawai aka ce ayi hakuri aje a haka tunda aure ya dauru? Don Allah ni dai ki fahimtar da ni wallahi kaina bai ta

ɓ

a kullewa irin yau ba, i am so confuse Khaleesat, Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un" Khaleesat dai ta sunkuyar da kanta duk tana jin abubuw

an da Safiyyah ke cewa tayi shiru hawaye na zuba idonta, Safiyyah ta kalli sama da sauri jin Footsteps, shiru tayi ganin Ajay ne ke saukowa downstairs, yana isowa cikin parlon ya kalli Khaleesat yace "Ai kinsan dakin da kike zama a gidan nan, so you can go

accommodate your self there" Yana fadin haka ya nufi inda zai yi leading dinsa to the kitchen of the house, Safiyyah ta bi sa da wani kallo, can ta ta

ɓ

e baki ta mike ta dau abincin Khaleesat tayi kasa da murya tace "Tashi mu je ki bani amsar tambayoyina,

ta yaya kika yarda da auren nan" Daga haka ta kama hannun Khaleesat dake goge hawayen da ke zuba idonta suka wuce sama zuwa Bedroom din da take zama idan tana gidan, suna shiga dakin wanda shi ma was sparkling clean Khaleesat ta ajiye handbag dinta kan gad

o cikin sanyin murya tace "Wanka zan yi Sophie, na gaji sosai" Safiyyah tace "To je kiyi bari in shigo maki da sauran kayan ki, amma wanne ne akwatin ki a kayan kar in ta

ɓ

o ma kaina masifa?" A hankali Khaleesat tace "Duk nawa ne kayan" Safiyyah tace "Atoh"

Sannan ta fita daga dakin, Khaleesat ta cire kayanta ta shiga bandaki, ko da tayi wanka ta fito har Safiyyah ta ciro mata kaya mara nauyi a tsadadden akwatin lefenta, da kayan shafanta, Khaleesat ta gama shiryawa sannan ta kwanta gefen gado tana kallon ab

incin da Safiyyah ta zuba mata, Safiyyah tace "To ki yi sallah mana sai ki ci abincin kafin ki kwanta" Khaleesat ta girgiza mata kai tace "I am not praying" Sai kuma ta sauko daga kan gadon ta zauna kan lallausan milk carpet din parlon ta jawo plate din ab

incin da Safiyyah ta dibar mata a hankali ta fara ci, ko da ta ci sake komawa tayi ta kwanta, ganin she looks so tired sai Safiyyah bata bukaci amsar tambayoyin da ta tula mata ba daxu ta kyaleta kawai, after some minutes bacci ya dauke Khaleesat. A hankal

i Khaleesat ta bude idonta ta fara kalle kallen dakin da take ciki, ita kadai ce a dakin bata ga Safiyyah ba, wuta mara haske sosai ne kunne a dakin which made her realize it's already dark, ta jawo handbag dinta a hankali ta ciro wayarta don ganin karfe n

awa, ta

ɗ

an bude ido ganin karfe goma saura few minutes, ajiye wayar tayi dai dai sanda aka bude kofar dakin, juya fuskarta tayi zuwa daya side din duk da bata san who open the door ba, after some seconds taga an kunna wutan dakin zuwa me haske tarr, zagaw

a yayi zuwa ta inda take facing a dakin suka hada ido, dauke idonta tayi, taji yace "Daki kike jiran a kawo maki dinner?" Without looking at him tace "Did I even say I am hungry?" Bai tanka ta ba ya juya ya nufi kofa ya fita daga dakin closing the door, mi

kewa tayi zaune tayi tagumi, ta fi minti talatin a haka sai kuma ta jawo wayarta ta bude WhatsApp, DM dinta da Jay ta shiga ta dinga kallon last message da ta ajiye masa da bai yi reply ba har yau, hawaye ta ji ya cika idonta, jiki a sanyaye tayi typing di

n sunan da take kiransa wato Housemate tayi masa sending, after a while ta kashe data dinta ta ajiye wayar don bata ga alamar yana online ba, komawa tayi ta kwanta tana goge hawayen dake sauka idonta.

*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jid

dah ur evidence 07087865788*

HALYSAAH

PAGE 10

7

Washegari har karfe sha biyu da kusan rabi Khaleesat na daki bata fita ba, tun da gari ya waye leg cramps yasa taki sauka daga saman gado banda wanka kawai da ta daure taje tayi ta canza kayan jikinta, ta

dade bata yi irin ciwon kafar ba idan tana period sannan ya hade mata da lower back pain, tana ta kwance tana jiran zuwan Safiyyah don tun da sassafe ta kirata don yi mata korafin jiya tayi tafiyarta tana bacci babu ko sallama, shine Safiyyah tace mata anj

ima zata shigo da rana, kofar dakin aka bude tayi saurin juyawa tayi backing kofar ta rufe ido don tun bai shigo dakin ba tasan shi ne saboda kamshin turarensa, ya zaga har inda take facing yace "Get up and leave this room Malama...." At first tayi niyyar

yin kmr bacci take but jin intonation da yayi using yayi maganar alamar he is not joking ta bude ido a hankali tana kallonsa, sosai ya hade rai yace "Ko baki ji na ne? You think i will tolerate you stressing my life in this House? Ni kike nufin zan kawo ma

ki breakfast daki ko kuma kin zo da cook or any worker from Nigeria ne da zai dinga girki yana kawo maki daki? Or are you a baby?? Who do you think you are here to stress with ur problem?" Ƙin cewa komai tayi, a fusace yace "Am i making any sense?" Dauke k

ai tayi ta tura baki tace "I am not feeling fine" Ya mata wani kallo yace "What is making you not to feel fine?" Shiru tayi taki cewa komai, yayi mata tsawa yace "Kee" Kamar zata yi kuka tace "To wai ba cramps bane, I am having leg cramps" Tana fadin haka

hawaye ya cika idonta, yace "And who did you tell that? Baki da phone number dina ne? Since you are a type of person that is always problematic from this problem to that problem, anytime any of ur so called problem arise don't you have my number?" Ita dai

tayi shiru bata ce komai ba, ya juya ya nufi bathroom din dake dakin wishing dama Yakumbo tana da Visa available da jirgi kawai zai biya mata ta taho ko zai samu rest of mind daga issues din yarinyar nan don bazai iya ba, gefe kawai zai koma ya zuba masu i

do yana kallo a gidan, after a while ya fito daga bandakin yana kallonta yace "Ko tasowar ma baza ki iya ba zuwa bandaki?" Ta juya ta kallesa, ganin his face is very serious ta mike zaune ta sauko da ƙafafuwanta daga saman gadon a hankali, daurewa tayi zat

a tashi amma ta kasa mikewa tsaye, ya nufi inda take zaune ya hade rai ya mika mata hannu, dauke kai tayi giving him her hand ta daure ta mike tsaye with his help, daga nan kuma ta zame hannunta ta fara tafiya a hankali tana rike waist dinta zuwa bandakin,

ruwa me zafi ba sosai ba ya cika mata a bath tub for Hot bath, suna hada ido bayan ta shiga bandakin ta kulle kofar, she felt so much relieve after the hot bath, after almost 40 minutes ta fito daga bandakin bayan ta maida kayan jikinta don kar ma ta fito

daure da towel ta gansa a dakin, bata gansa dakin ba sai tray din abinci dake ajiye kan Carpet with some fresh fruits a bowl, wani kayan ta dauko a akwatin ta, bayan ta gama shafe shafenta ta saka kayan ta dau hularta ta saka, abincin da aka ajiye mata ta

bude tana dubawa taga ko kadan ba shi da yawa kamar dai yanda turawa ke cin abinci, hakan ma yayi mata don da yana da yawa ma bata san yanda zata yi da shi ba tunda English breakfast ne da bai dameta ba, baked bean da aka yi micro waving sai omelette a ge

fe with few slices of bread da aka yi toasting and 2 sausage, sai hadin salad madaidaici a wani bowl wanda iya olive oil aka yi drizzling a kai, ta dau pain reliever dake kan tray din da goran ruwa ta ajiye su gefe sannan ta fara hada shayi don har da gwan

gwanin madara da Milo da cube din sugar ya ajiye mata, sai da tayi breakfast din sannan ta sha maganin, iya apple kawai ta ci a fruits din, after 15 mins ta mike zata fita da tray din don taji saukin cramps din ta samu relieve sosai, tana sauka downstairs

ta gansa zaune parlor yana kallon TV at the same time yana operating wayarsa, bai kalli direction dinta ba har ta wucesa zuwa kitchen sannan ya juya ya bi ta da kallo har ta shiga kitchen din, bayan ta gama wanke utensil din da ta kai kitchen ta goge wajen

sink din ta fito daga kitchen din dai dai sanda aka bude kofar parlon da sallama suka yi ido hudu da Safiyyah dake leko cikin parlon daga waje kamar mara gaskiya, sai kuma ta shigo parlon don sun hada ido da Ajay, Tana yake hade da sosa keya tace "Good af

ternoon" Sau daya ya kalleta ya dauke kai yace "Evening" Khaleesat taji dadin ganin frnd din nata ta karasa har inda take tace "Sannu da zuwa Sophie" Hannunta ta kama zuwa sama, ya bi su da kallon gefen ido yana ci gaba da danna wayarsa, suna shiga daki Kh

aleesat ta kulle tana kallonta tace "Kawai sai ki tafi jiya baki tasheni ba" Safiyyah ta sauke ajiyar zuciya tace "Wallahi da ke na kwana a rai Khaleesat, my head still can't process what you told me yesterday, ganin abun nake kamar Movie fa, dama ana migr

ating aure?" Khaleesat ta kamo hannunta murya a sanyaye tace "Don Allah kina ganin akwai mafitar da zaki bani akan wannan auren Sophie? Wallahi har cikin raina ni dai bana son auren, ni ban ce ina sonsa ba aka aura min shi, hasali ma ban sani ba don babu w

anda ya gaya min sai bayan aure da aka kai ni Bauchi na sani, we can never be compatible with him Safiyyah cause he is not my type and i am not his type too, i wish gidan Abdul ma na koma da wannan auren, i am soo heartbroken...." Tana kuka a hankali ta ka

re maganar tana kallon Safiyyah, Safiyyah ta rike ha

ɓ

a tace "Gidan Abdul? Eh lallai har yanxu baki da hankali kuma bana tunanin zaki yi, wallahi ba don Housemate ba da dai ki koma ma Abdul gwara maki Ajay din ki lallaba kiyi maneji da shi duk da kusan jirg

i daya ya kwaso su da Abdul din kawai shi dai nasan bazai jibge ki yanda Abdul ke yi ba, amma duk same categories ne su biyun birds of the same feather, shi wannan ga shegen renin hankali da maida mutum

ɗ

an iska, kina ji fa yanxu nace masa Good afternoon y

a mayar min da evening, karfe biyun rana ne evening idan ba walakanci ba? Sau uku kenan yana min wannan iskancin a garin nan ina lissafawa bai sani ba, To wai wani irin al'amari ne wannan ya ja har aka daura aure da shi ne Khaleesat don nasan ba

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login