Showing 291001 words to 294000 words out of 641791 words

Chapter 98 - HALYSAAH COMPLETE

yana jujjuya Birthday card din hannunsa yace "But you are his boss not his friend...." Sai kuma yayi murmushi yace "This is soo

thoughtful of Paul, few months back ba ka basa kudi masu yawa ba, yana da hankali sosai ai" Gently Jay ya bude turarurrukan duk ya fesa daya bayan daya to perceive the scent, ya lumshe ido don kamshin sun tafi da shi, yace "This is waow" Lokaci daya kamsh

i ya cika motar gaba daya, Shi dai Ajay bai ce komai ba ya bude motar ya sauka, Jay ya maida duk gifts din cikin box sannan ya fito daga motar yana rike da su ya kulle motar, suka nufi cikin gidan.... Karfe tara saura Ajay ya dau laptop dinsa da waya zai w

uce daki yana kallon Jay da Cousin Bro dinsu Mukhtar yace "Good night" Sannan ya wuce dakinsa, kulle dakin yayi da makulli ya ajiye laptop dinsa ya zauna gefen gado yayi dialing number Khaleesat, Khaleesat na zaune tare da Nenne a dakin da Nenne ta zabar m

a kanta a gidan, Islam ta shigo da wayar Khaleesat a hannunta ta mika mata tace "Aunty ana kiran ki" Amsan wayar tayi tana duba me kiranta ganin Ajay ne ta mike don dama ta gaji da zancen da Nenne ke mata, fita tayi daga dakin tayi picking call din ta kai

kunne tace "Good evening" Yace "Ke... Ni na aikeki ki siya min Birthday present? Who sent you message? A ina kika samu wannan kudin da kika siyo turaren nan?" Khaleesat dake ta sauraronsa ta kyabe baki tace "For once kayi acting like how every other person

will do, kawai godiya zaka min for getting u a present and Birthday card, shikenan...." Yace "To bana so, zan kuma bada a maida maki kayanki" Ɗan murmushi tayi tace "Ka maido min da kudin dai...." Katse wayar taji yayi, ta ta

ɓ

e baki, dama tasan he will ne

ver change kuma ko kadan bata ji haushin abinda yayi mata ba, in ma bai yi bane zata yi mamaki, although she sees him as the senior brother she never had, shi yasa bata jin haushinsa ko kadan, ko barin wajen da take tsaye bata yi ba sai ga Alert din 1M ya

shigo wayarta, dakinta ta tafi ta zauna ta dinga dariya kamar ta

ɓ

a

ɓɓ

a, wato har da riba ya kara mata a kai, kamar ta kirasa tace saura Birthday Card din yaushe za a maido mata kawai dai ta kyalesa ta bar wayar a daki ta fita parlor, yaran Mama Shatu ne zau

ne kasan tiles din parlon suna kallo tunda Nenne ta hanasu zama kan Carpet wai kar yayi datti, Nenne ta fito dakinta tace "Ace har karfe tara Ali yaki shigowa gidan nan, yana can zaune kofar gida kan benchi wani ba sai yace Mai gadi bane" Ita dai Khaleesat

bata ce komai ba don tun dawowarsu gidan har yanxu fa Babanta dari dari yake, yaki sakin jiki da gidan, in yana unguwan to a kofar gida zaka samesa zaune kan Benchi da ya sa kafinta ya buga masa, Nenne tace "Wannan ai salon ya ja mana kallon raini ne a un

guwan nan, sai ya nuna ma kowa talakawa ne mu kyauta aka bamu gidan nan sannan hankalinsa zai kwanta, kwata kwata yaki sakin jiki yayi kamar shi ne Mai gidan da ya gina gidan" Khaleesat ta koma daki ta dau mayafinta ta fita compound, ita kanta she is feeli

ng somehow yanda Babanta yaki zama comfortable a gidan, da alama babu yanda ya iya da mahaifiyarsa ne yasa ma yake gidan nan, one thing about her father is bai yarda mutum yayi maka gagarumin kyauta babu wani dalili me karfi ba, shi yasa har yau bai sake y

ayi na'am da gidan ba, don yace bai san dalilin siyan gidan ba, kamar kullum yana zaune kan Benchi da karamar wayarsa da yake kunna Radio yana saurare ga carbi a hannunsa yana ja, ya juya jin an bude gate, Khaleesat ta karasa ta zauna daga gefensa tana kal

lonsa tace "Baba bbu sauro a nan kuwa?" Malam Ali yace "Ai shi yasa na saka Safata Jiddah, sauro kam ai ba a rasa su a ko ina" Khaleesat ta

ɗ

an yi murmushi tace "Amma Baba me yasa baka son ka dinga shiga ciki sai dai kawai ka shiga idan dare yayi sosai, da

sassafe kuma ka fita kasuwa" Malam Ali yayi murmushi yace "To ai zaman gida na mata ne Jiddah, ni yaushe zan ta zama a cikin gida tare da mata" Sauke idonta tayi cikin sanyin murya tace "Baba ka kwantar da hankalinka plss, tsakaninsa da Allah ya bamu gida

n nan ba don wata manufa ba, trust me pls" Malam Ali yayi wani murmushin ya jinjina kai yace "Ke yarinya ce har yanxu Jiddah, haka kawai babu wani dalilinsa bazai siya mana wannan gida me tsada da komai na more rayuwa a ciki ba, babu yanda na iya da Baabat

a ne amma wannan gida ba gidan da za mu saki jiki a cikinsa bane mu zauna don komai zai iya faruwa in ma yanxu in ma nan gaba, shi yasa ma nayi amfani da wannan dama wajen fara gyaran gidanmu da muka baro a Mariri tunda babu kowa ciki, yanxu haka har an fa

ra plaster a kasa, kuma duk za a canza zinc din gidan da Ceiling, sannan a kara girman window din dakunan, a fitar da inda ruwa zai dinga fita ya dena taruwa cikin gidan, duk abokaina na can ni bance masu gida aka siya min ba, na dai ce an bani gida in zau

na har zuwa sanda zan gama gyara nawa gidan na Mariri" Khaleesat ta kasa cewa komai, amma duk jikinta yayi sanyi sosai, tasan bata da wani kalman da zata sake using wajen convincing Babanta, don his belief will be his belief, ita dai tasan daga

ɓ

angaren Ho

usemate dinta baza a ta

ɓ

a samun matsala akan gidan nan ba balle tuni ya basu takardun gidan da komai, wasu motoci uku ne suka shigo layin a jere, Malam Ali da Khaleesat suka juya suna kallon motocin da suka dallaro masu hasken fitila, amma lokaci daya duk

aka kashe fitilun motar masu haske wanda da alama saboda su aka yi hakan, haka kawai Khaleesat taji gabanta na faduwa barin da taga motocin all halted at the same time a kusa kusa da su, Malam Ali dai ya gyara zama har sannan yana kallon motocin shi ma, af

ter almost 2 minute da tsayuwar motocin, motar dake gaba wani ya bude ya sauko daga front seat da alama dai Security ne, ya bude back seat wanda ke bayan motar ma ya sauko, Malam Ali dai sai kallonsa yake don kara tabbatar da shi din yake gani ko ba shi ba

, can ya kalli Khaleesat yace "Tashi ki shiga ciki Jiddah" Gaba daya hankalin Khaleesat ya gama tashi ta girgiza kai tace "A'a baba I will remain here" Guard din mutumin na biye da shi a baya ya nufo Malam Ali da murmushi fuskarsa ya kai masa hannu yace "A

ssalamu alaikum Alhaji Aliyu" Malam Ali ya mike ya kai masa hannu yana mamakin me kuma ya hadasa da Deputyn garin nan, Khaleesat dai bata ma ganesa ba amma ta mance rabon da ta shiga tashin hankali irin na wannan moment din, me zai kawo su wajen Babanta da

daddaren nan da motoci har uku, Deputy ya kalleta yace "Sannu yarinya" Dakewa tayi ta gaishesa ya amsa da fara'a sannan ya maida dubansa kan Malam Ali yace "Idan babu damuwa Alhaji Ali mun zo maka ne akan wani batu me muhimmanci, Allah yasa zaka bamu loka

cinka ka saurare mu, in kuma lokacin da za mu dawo zaka saka mana to duk babu damuwa" Malam Ali yace "To ni dai Allah ya sa lafiya ranka shi dade" Deputy yace "Babu komai sai Alkhairi ka kwantar da hankalin ka, ni da abokina ne da sauran manyan mutane muka

zo har inda kake muka same ka akan wannan batu da ke tafe da mu, amma sai dai muna baka hakuri mun maka zuwan bazata, and this could be sort of inconvenient....." Malam Ali ya dake don zuwa yanxu kam ya gama ƙaguwan yaji me kuma ya hadasa da manyan mutane

kamar yanda Deputy yace, sannan me ya kawo Deputy da kansa inda yake, a ina ma ya san sa?? Duk da yasan Deputy mutumin kirki ne kuma kowa ya shaida amma fa hankalinsa yaki kwanciya, yana gyada kai cikin karfin hali yace "A'a ba komai ranka shi dade, bari

a shimfida tabarma sai mu zauna a nan tsakar gida, hakan yayi ko?" Deputy yace "To babu laifi Alhaji Ali" Malam Ali ya kalli Khaleesat yace "Shiga ciki ki shimfida mana tabarma a compound Jiddah" Mikewa Khaleesat tayi jiki a sanyaye ta shiga cikin gidan do

n yin abinda Babanta yace tayi....

*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah*

07087865788

H

ALYSAAH

PAGE 9

1

https://chat.whatsapp.com/B5uR4Jfj6fZIIN0EIIHegM?mode=ac_t

Bayan Khaleesat ta shimfida tabarmin da Babanta yasa ta shimfida

ta koma parlor ta nufi kujera zata zauna har a lokacin hankalinta ya kasa kwanciya duk da irin approach din deputy toward her dad but she was so tense and confused, gashi ita bata ma san ko su waye ba, Nenne na kallonta har ta zauna kan kujera sannan tace

"Yanxu baki lallabasa kun shigo gidan tare ba kika bar sa zaune bakin gate? Haka rayuwa zata ci gaba yana zaman kofar gida kamar Mai gadi kenan?" Ita dai Khaleesat bata ce komai ba, she was trying all possible best to keep calm at this moment, Nenne ta kya

be baki ta dau remote ta danna inda Islam ta nuna mata ana dannawa idan za a canza tashan kallo, tana canza tashar duk yaran dake zazzaune parlon suka juyo suna kallonta, ta tsuke fuska, Mikewa Khaleesat tayi ta bar parlon ta tafi dakin Ummanta ta sameta z

aune tare da Aunty Farida sai Mama Shatu dake zaune daga kusa da kofar dakin a zuwan ta shigo hira da Umma, tunda Khaleesat ta shigo Umma ke kallonta, ganin Mama Shatu kawai Khaleesat ta juya ta tafi dakinta, Aunty Farida ma ta bi ta da kallo, bayan kusan

minti biyar sai ga Umma ta shiga dakin nata tana kallonta tace "Lafiya Khaleesat?" Khaleesat ta sauke idonta har Umma ta karaso ta zauna gefen gado tana kallonta, sai ga Aunty Farida ma ta shigo dakin tana tambayarta me ya faru? Da kyar Khaleesat tace "Bab

a ne yayi baƙi a motoci ban san daga ina suke ba" Umma ta kasa daina kallonta ita ma a

ɗ

an tsorace tace "A motoci kuma? Ke wa ya gaya maki?" Khaleesat tace "Muna zaune tare a waje sai ga su a motocin" Hankali tashe Umma tace "Yanxu yana ina Malam din?" Kha

leesat tace "Ya ce in shimfida masu tabarma a tsakar gida, har ma sun gaisa da baƙin" Juyawa Aunty Farida tayi ta fita daga dakin, ta tafi can compound ita ma dai hankalinta a tashe, ai ko ta hangosu zazzaune saman tabarma su hudu sai Malam Ali na biyar da

ya sinne kai ko me suke gaya masa oho, ta juya ta koma cikin gida. Karfe goma saura na daren Khaleesat ta shigo parlon Babanta tare da Aunty Farida, Umma ma na zaune parlon sai Nenne, Nenne ta gyara zama tace "To yanxu Ali ko don wannan girmama ka da yan

unguwan nan suka yi suka shigo har gidan nan suka zazzauna a tabarma suna gabatar maka da kansu ya kamata ka rufa mana asiri kar ka sake zama bakin gate kamar Mai gadi, baka ji dadin da naji ba wallahi ganinka a tsakankanin manyan mutane a tsakar gida" Mal

am Ali dai kallonta kawai yake, can yace "Yanxu Baaba wa yace maki yan unguwan nan ne?" Nenne ta saki baki tace "Ba yan unguwan nan bane? To yan unguwan dake gaba da namu ne ko wanda ke bayan namu?" Malam Ali yace "Ni baƙin da suka zo gidan nan bama su da

alaka da unguwan nan gaba dayan ta" Nenne ta zaro ido tana kallonsa tace "Kai haba dai? To a ina ka samo su Ali? Su waye?" Malam Ali ya sauke ajiyar zuciya yace "Dalilin tara ku a nan da nayi kenan Baaba, duk za ku ji waye su da kuma me ya kawo su gidan na

n" Nenne ta gwalo ido tace "Wani laifin kuma ka sake yi Ali? Mun shiga uku mun lalace, abun arziki bai amshe mu ba, ko kwace gidan suka yi?" Malam Ali ya kara sauke wata ajiyar zuciyar cikin nutsuwa ya fara koro masu bayanin su waye mutanen da suka zo da k

uma dalilin zuwan nasu gidan, tunda ya fara magana Khaleesat ke kallonsa babu ko kiftawa zuciyarta na bugawa, haka ma Umma da Aunty Farida that look speechless, Sai da Nenne ta jira ya kai har karshe sannan tayi mitsi mitsi da ido tace "Amma ka ban mamaki

kuma ka ban tsoro da baka masu koran kare ba Ali, anya kuwa ba a canza min kai a daki na je wankan jegon ka a ban

ɗ

aki ba kuwa tunda gidan yawa ne kuma mu uku muka haihu ba wani tazara tsakaninmu??? Ali yanxu kana nufin baka kore su ba ka zauna ka sauraresu

har karshe?" Malam Ali yace "In kore su kuma Baaba? Na fa gaya maki su wa da su wa suka zo, ta yaya zan koresu fisabililahi?" Nenne ta mike a fusace tace "To ina ruwana da koma su waye, kai ko shugaban kasa ne in ya gaya maka abinda bai gamshe ka ba ai za

ka kama kanka balle ma ba shi bane, yanxu a takaice kana nufin ce masu kayi toh shikenan?" Malam Ali yace "A'a, ni ban ce masu haka ba Baaba...." Nenne tace "Amma daga Awdul din har iyayensa Allah Ubangiji ya tsine masu albarka daga su har wanda ya basu sh

awaran turo maka manyan mutane su baka hakuri, kai kuma da yake gantalalle ne kai baka san ciwon er ka ba maimakon kace masu ai an sa mata rana biki saura sati daya yanxu haka shine ka zauna da wata safarka a kafa kamar

ɗ

an bigilantee a tsakankaninsu kana

sauraronsa, to wallahi idan ban kai karar su kotu ba Allah ya tsine min, ko Awdul ne ka

ɗ

ai namiji da ya rage a duniya idan na kara basa auren jikata a kirani tsohuwar banza tsohuwar hofi, haba fisabililahi, sannan shi yaron nan da ya siya mana gidan nan ka

nin ubanmu ne shi ko na uwarmu da zai siya mana katon gida haka idan har ba sonta da aure yake ba, sai ya fito ya gaya mana yana sonta mu wani irin ƙwaƙwalwa gare mu da baza mu gane ba? ai ni ba yarinya bace nasan abinda nake, wallahi sonta yake so kuma na

aure, haka kawai ka biye barayin gwamnati su saka ka a tsakiya don su tsorata ka ka sake daukar er ka ka bada a karo na biyu? Ko dai baka da lafiya ne Ali?" Malam Ali dake ta kallonta cikin nutsuwa yace "Yanxu fa Baaba baki saurareni na kai karshen bayani

na ba...." A fusace tace "To ina jin ka maza maza tafi karshe" Malam Ali yace "Ni nace masu bazan ma Jiddah dole ba, duk abinda take so shi zan mata kuma shi nake so, in ma shi Abdul din tace take son komawa ni bazan hanata ba sai dai in bi ta da fatan al

khairi, in kuwa tace bata so to hakan ya zauna don bazan mata auren dole a karo na biyu ba" Nenne tace "To maza tun basu yi nisa sun isa gida ba ka bi su kace ai babu wannan zancen ko makamancin sa, yarinya tace bata sonsa ta tsanesa, in kuma wannan karan

da karfin mulki za su yi amfani da shi wajen auren nata kamar yanda suka yi da kudi watannin baya to sai su yi mu gani, maza su gaya ma

ɗ

an su ya cire shegun idonsa akan Khaleesah bata sonsa kuma tafi karfinsa nesa ba kusa ba wallahi" Hawaye ne kawai ke zu

ba idon Khaleesat tana shessheka tana jin wani zafi a ranta, ta jinginar da kanta jikin Aunty Farida cause she is beginning to loose her control, Sosai Aunty Farida ke jin dadin maganganun Nenne don ita ma banda tafarfasa babu abinda zuciyarta yake a inda

take zaune, Umma kuwa dafe kanta da yayi mata nauyi sosai tayi, Nenne tace "Ka ji me nace maka ko baka ji ba Ali?? Tun gari bai waye ba ka san yanda zaka yi ka sanar masu babu wannan maganar da suka zo da shi don har an saka ma Khaleesah rana da wanda take

so kuma ranan jama'ar nan daurin aure" Malam Ali yace "Shikenan Baaba, su a yanda suka zo ma suna tunanin bayan sun gabatar da bukatarsu nauyin su da ganin girmansu zai sa in amince lokaci guda babu ja in ja, amma wallahi ban yi haka ba, nuna masu nayi ni

bani da ta cewa sai abinda 'ya ta tace shine magana don bazan kara mata dole ba, yanxu zuwa gobe suna saurarata su ji ya ake ciki, don haka bazan boye masu komai ba in sha Allah, zance su yi hakuri nayi mata miji" A fusace Nenne ta nufi kofa tana cewa "In

Alhaji Musa bai yi hankali ba zan taka har gidan nasa in ci masa mutunci wallahi, tun da saboda shegen

ɗ

an sa aka halitto Khaleesah ba sai ya zo ya sake daura auren ba mu gani, wato ya zo maka da manyan mutanen garin nan yanda zaka yi masu biyayya ga ka

ɗ

an banza ko? To mu zuba da su"

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login